Za a shirya fim kan makalewar yara a kogon Thailand

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Masu aikin ceto na daukar yaran a kan gadon marasa lafiya

Za a mayar da kogon nan da yara 12 suka makale a ciki a arewacin Thailand fiye da mako biyu, gidan adana kayan tarihi.

Masu aikin ceto sun ce gidan adana kayan tarihin zai nuna yadda aikin ceton ya fara, inda ake sa ran zai zamo "babban wajen" da zai jawo wa kasar 'yan yawon bude ido.

A kalla kamfanoni biyu suna neman yin fim din wanda zai bayar da labarin yadda ceton yaran ya kasance.

A yanzu dai tawagar yaran da aka ceto din duk suna asibiti don murmurewa.

An saki wani bidiyo da ke nuna su cikin halin lafiya, duk da cewa za a ci gaba da kebe su a asibiti tsawon mako guda.

Rundunar sojin ruwan Thailand ta fito da bidiyon aikin ceton da kanta, da ke nuna yadda kwararrun masu ninkaya suka taimakawa tawagar 'yan kwallon kafar na Wild Boar ta hanyar tafiya mai cike da hadari a cikin kogon.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bidiyon yadda yaran ke farfadowa a asibiti

A ranar Alhamis, an yi wa rundunar sojin ruwan da suka zo daga kasashen waje maraba, a yayin da suka sauka a filin jiragen saman soja a kudancin babban birnin kasar Bangkok.

Me zai faru da kogon?

Kogon Tham Luang yana daya daga cikin manyan kogona a Thailand. Yana tsakanin wasu tsaunuka ne da ke kewaye da garin Mae Sai, a lardin Chiang Rai a arewacin iyakar kasar Myanmar.

Babu wani ci gaba a yankin, kuma babu isassun wuraren yawon bude ido.

Narongsak Osottanakorn, tsohon gwamnan ne kuma shugaban aikin ceton, ya yi jawabi a wani taron manema labarai, inda ya ce: "Yankin zai zama gidan adana kayan tarihi, don nuna yadda aka gudanar da aikin ceto yaran."

"Za a kafa wata mattarar bayanai mai mahimmanci kuma zai zama wata babbar hanyar jawo hankalin masu yawon bude ido da zai samar da kudaden shiga ga Thailand," a cewarsa.

Duk da haka, Firai ministan kasar Prayuth Chan-ocha ya ce za a samar da kariya a ciki da wajen kogon sosai don kare masu yawon bude ido.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Labarin 'yan samarin ya jawo hankalin duniya

Ba a bayyana ko idan an bude gidan adana kayan tarihi ko zai dinga aiki duk tsawon shekara ne, saboda yadda ake yawan samun ruwan sama mai yawa da ke jawo ambaliya a Thailand.

Ruwan sama kamar da bakin kwaryar da aka sheka ne ya yi sanadin makalewar 'yan mazan a cikin kogon mai zurfi a yayin da suka shiga don neman ilimi.

Masana'antar Hollywood

Kamfanin samar da fina-finai biyu suna rige-rigen mayar da labarin tashin hankalin da yaran suka shiga zuwa fim.

Tun kafin ma a fitar da mutum 13 din, kamfanin shirya fina-finai na Pure Flix na Amurka - masu shirin fina-finai na Kiristoci - ya sanar da cewa masu shirya fina-finansa suna hira da masu ceto don jin ta bakinsu kan yadda al'amarin ya gudana.

Wanda ya kafa kamfanin Michael Scott, wanda ke zama a kasar Thailand, ya ce matarsa ‚Äč‚Äčtare suka taso da Saman Gunan, tsohon sojan ruwan da ya rasa ransa a lokacin aikin ceton.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce: "Ganin irin jarumtar da aka nuna a cikin kogon, da kuma fiddo da dukkan masu ninkayar da rai, wani abu ne mai sa tausayi da taba rai." in

Amma a cewar kamfanin shirya fina-finai na Ivanhoe da ke birnin Los Angeles, shi gwamnatin Thailand da rundunar sojin ruwan kasar suka zaba don yin fim.

Kafofin watsa labarai na Amurka sun ruwaito cewar Jon M Chu ne zai ba da umarnin fim din. Shi ne ya yi hadin gwiwa da kamfanin Ivanhoe wajen bayar da umarni a wani fim da za a saki nan gaba mai suna 'Crazy Rich Asians.'

Tuni mutane sun fara nuna damuwa a kafofin sada zumunta kan yadda kamfanonin fina-finan za su fi bayar da fifiko ga 'yan kasashen wajen da suka taka rawa a aikin ceton fiye da 'yan kasar ta Thailand.

Sai dai Chu ya dage cewa fim din zai yi adalci.

A ranar Asabar 23 ga watan Yuni ne wasu 'yan samari 12 tare da kocinsu suka shiga kogo inda suka makale bayan da ruwa mai tsanani ya jawo ambaliya.

Masu ninkaya na Burtaniya ne suka gano su bayan da aka shafe kwana tara ba a gansu ba, kuma daga baya an ceto su a wani aiki da ya hada da gwamman kwararrun masu ninkaya da kuma daruruwan masu aikin ceto.

Labarai masu alaka