Wasu matan Najeriya 'sun gigice' da son auren Dangote

Dangote Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sau biyu attajirin yana aure

Mata da dama a Najeriya suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu bayan wani labari da jaridar Financial Times (FT) ta wallafa, inda ta bayyana cewa mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote "yana neman matar da zai aura."

Wannan ya sa wadansu mata musamman a kafafen sada zumunta suka rika bayyana bukatarsu ta neman auren attajirin, wanda yanzu ba shi da mata.

Sai dai wasu daga cikin masu sharhi kan lamarin sun ce ba a fahimci ainihin zancen attajirin ba, don a cikin kalaman da ya yi wa jaridar ta FT, bai fito kai tsaye ya ce yana neman matar da zai aura ba.

Ko ita ma jaridar ba ta sanya wannan magana a matsayin kanun labarin nata ba, sai dai wasu jaridun da suka dauki labarin ne suka sanya hakan a matsayin kanunsu.

"Shekaruna suna kara ja. Shekara sittin ba wasa ba ne...babu amfani na fita neman (aure) kuma idan ka samu ba ka da lokaci," in ji Dangote kamar yadda ya bayyanawa jaridar.

Ya ci gaba da cewa: "A yanzu haka abubuwan da suke gabana suna da yawa matuka, muna da matatar mai da kamfonin takin zamani da bututan iskar gas. Ya kamata na natsu," in ji shi.

Aisha Falke mai shafin Instagram na northern_hibiscuss ta wallafa labarin Dangoten kuma ta shaida wa BBC cewa ta samu dimbin sakonni daga mata wadanda suke namen attajirin ya aure su.

Aisha ta kara da cewa: "Tun a ranar da na sanya labarin a shafina, mata suke ta turo min sakonni har da kiran waya, cewa na yi musu hanya.

"Sun yi tsammanin ko ta wajena ya zo neman auren, ba su san cewa ba ni da ko wacce irin alaka ko kusanci da Dangote ba, labari kawai na gani na sanya musu."

Ga ra'ayoyin wadansu mutane da muka samu da shafin Instagram a Najeriya:

zakiyamusajibril "Tirkashi ai har sai ya rasa wadda zai zaba don zai samu issasun masoya."

khaxeenerh_yaree "Tou ta ina ake samo shi ๐Ÿ˜‚bai ba da inda za'a same shi ba."

jrabdulmalik "Sir can I apply for my sister now because she's not online now...she already have four years marriage experience, I already filled it to divorce on her ever since your vacancy come up๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ"

Wannan cewa ya yi zan iya nema wa kanwata(aurensa) don ba ta kan Intanet yanzu...tana da gogewa kan zaman aure na tsawon shekara hudu, na bukace ta da ta kashe aurenta tun bayan da na ji labarin nan.

Sai dai kuma akwai wadanda suka yi wa attajirin addu'a da kuma ba shi shawara, kamar haka:

hafcerthassan: "Allah ya ba shi ta gari wacce za ta so shi tsakani da Allah."

Wasu majiyoyi masu karfi dai sun tabbatar da cewa hamshakin attajirin ba shi da mata a yanzu, sai dai ya taba aure sau biyu kuma yana da 'ya'ya mata guda uku da duk suka yi aure.

Labarai masu alaka