Ban iya karatu da sauri ba – Buhari

Shugaba Buhari da Cyril Ramophosa
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari da Cyril Ramaphosa na kasar Afrika ta Kudu

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya karbi bakuncin takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa.

Shugaba Buhari ya bai wa masu sukarsa wata kafa wadanda suke kiransa "Baba mai tafiyar hawainiya" bayan ya amince cewa ya kasa sa hannu kan yarjejeniyar yin kasuwanci ba tare da shinge ba na nahiyar Afirka, saboda "ba ya iya karatu da sauri."

Shugaba Buhari ya ce yana da aniyar sa hannu kan yarjejeniyar da shugabannin Afirka suka rattaba hannu a kai a kasar Rwanda a watan Maris, nan ba da jimawa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ruwaito cewa a taron manema labarai da aka yi a ranar Laraba, Shugaba Buhari ya ce: "Ina son na tabbatar an ci ga da samun guraben ayyukan yi da kayayyaki a cikin kasarmu, ya kamata mu yi taka tsan-tsan kan yarjeniyoyin da za su sa a rika gogayya da watakila samun nasara kan masa'antunmu masu tasowa."

"Ba na iya karatu da sauri, watakila saboda ni tsohon soja ne. Ban karanta yarjejeniyar cikin sauri ba, kafin jami'aina suka ce ya kamata na sa hannu.

Ya kara da cewa "Na ajiye takardar kan taburina. Kuma zan sa hannu a kai nan ba da jimawa ba."

Shugaba Buhari na magana ne lokacin da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kai ziyara kasar.

Tun farko Mista Ramaphosa ya fada wa 'yan kasuwa 'yan Najeriya cewa akwai wurare da dama da kasarsa za ta amfana daga yarjejeniyar kasuwanci ba tare da shinge ba, kuma ana kan nazari kan daftarin doka da zai ba mutane damar zirga-zirga daga wani yanki zuwa wani yanki.

Wannan ita ce ziyarar Mista Ramaphosa ta farko zuwa Najeriya tun bayan da ya zama shugaban kasa a watan Fabrairun da ya gabata.

Ya ce kasar Afirka ta Kudu na son ta karfafa alakar da ke tsakaninta da Najeriya. Kasashen biyu su ne suke da tattalin arziki ma fi girma a Afirka.