Buhari ya yi Allah-wadai da harin Sokoto

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal Hakkin mallakar hoto TAMBUWAL/FACEBOOK
Image caption Gwamna Tambuwal ya ce akwai gazawar shugabanci ga yawaitar kashe-kashe a Najeriya

Mutane na gudun hijira daga kauyukan da aka kai hari a gundumar Gandi cikin karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

A ranar Litinin ne wasu 'yan bindiga suka kashe mutane sama da 30 a kauyuka da dama na gundunar Gandi da suka hada da Kursa da Alliki da Kari da Warwanna da Tabanni.

Cikin wadanda aka kashe har da hakimin kauyen Tabanni.

An binne gwamman mutanen da aka kashe a hare-haren.

Hakkin mallakar hoto WhatsApp

Wasu mazauna Gandi sun shaida wa BBC cewa mutane na kauracewa gidanjensu a kauyukan da aka kai hare-haren saboda tsoron ana iya sake kai hari.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a kauyukan.

A cikin sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce "gwamnatinsa ba za ta amince da wadannan kashe-kashen rayukan mutane ba kuma muna aiki a kullum domin gano wadanda suke tallafa wa hare-haren."

Shugaba Buhari ya ce "wannan gwamnati ba za ta yarda da wannan mummunan tashin hankalin ba, kuma muna aiki a kowane lokaci don gano mutanen da suke tallafa wa wadannan hare-haren."

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Sokoto, a cikin wata sanarwa ya daura laifin yawaitar kashe-kashen mutanen da ake samu kan gazawar shugabanci daga bangaren gwamnatin tarayya.

Gwamnan ya ce akwai bukatar a sake duba tsarin tafiyar da tsaro a Najeriya saboda yadda rayuka ke salwanta a sassan kasar.

"Za a iya magance dukkanin kashe-kashen da ake samu, amma saboda akwai gazawa ta shugabanci. Najeriya ba za ta ci gaba ba kuma ba za ta kasance cikin wadanda suka ci gaba ba a karni na 21 a irin wannan yanayi na haifar da masu zaman makoki kusan a kowace rana." in ji Tambuwal.

Sai dai kuma a cikin sakonsa na jaje ga mutanen Sokoto, Shugaba Buhari ya jaddada wa 'yan Najeriya cewa tabbatar da tsaronsu ne babban muhimmin abin da gwamnatinsa ta damu da shi.