Wata sabuwar cuta da 'ba ta jin magani' ta bulla

  • Daga Michelle Roberts
  • Editan al'amuran da suka shafi lafiya na BBC
A person pulling a condom out of their pocket
Bayanan hoto,

Kororon roba

Kwararru sun yi gargadin cewa wata cuta da ake kamuwa da ita ta hanyar jima'i za ta iya zama sabuwar cutar da ba ta jin magani idan mutane ba su dauki matakan kariya ba.

Cutar da ake kira Mycoplasma Genitalium (MG) ba ta da alamomi, amma za ta iya haddasa ciwon mara, wanda zai iya sa mace ta kasa samun juna biyu.

Ba lalle ba ne mutum ya san yana dauke da cutar MG - kuma idan ba a dauki matakan da suka kamata ba, to za ta iya komawa cutar da ba ta jin magani.

Kungiyar kula da ciwon sanyi da kuma HIV ta Birtaniya ta kaddamar da wani sabon tsari.

Kaidojin da ta fitar sun yi bayani dalla-dalla kan yadda mutum zai gane yana dauke da cutar da kuma maganin da ya kamata a sha.

Shin mecece cutar MG?

Mycoplasma Genitalium wani nau'in kwayar cutar Bacteriya ne da ke sa ciwon mafitsara a maza, abin da ke sa suna jin ciwo idan suna fitsari tare da fitar da wani miki.

A jikin mata kuma, kwayar cutar na sa ciwon mara (a mahaifa da kuma kunnen mahaifa) da zazzabi da kuma zubar jini a wasu lokutan.

Ana kamuwa da cutar ta hanyar yin jima'i ba tare da kororon roba ba da mai dauke da cutar. Kororon roba yana hana yaduwar cutar.

A shekarun 1980 ne aka fara gano cutar a Birtaniya kuma ana kyautata zaton ta shafi kashi daya zuwa biyu na al'ummar kasar.

Cutar MG ba ta cika bayyana alamominta ba, kuma ba ko yaushe ne ake bukatar magani ba.

Amma za a iya yin kuskure wajen bayyana cutar a matsayin ciwon sanyi da ake kamuwa da shi ta hanyar jima'i da ake kira Chlamydia.

Kungiyar kula da ciwon sanyi da kuma HIV ta ce wannan abin damuwa ne.

An dai kirkiro da nau'rar gwajin cutar MG.

Sai dai babu su a asibitoci kodayake likitoci a Birtaniya za su iya tura da samfurin gwaji zuwa dakin gwaji na gwamnati domin samun sakamako.

Za a iya ba da maganin Antibiotics - sai dai cutar na bijirawa wasu magunguna.

'An gano ina dauke da cutarMG'

John - ba shi ne sunansa na asali ba - ya tuntubi BBC domin ya ba da labari kan yadda ya rika fama da cutar.

"A bara ne aka bayyana cewa ina dauke da cutar bayan na hadu da sabuwar budurwata."

"Dukanmu mun je an yi mana gwaji kuma an ce babu wata cuta tare da mu lokaci da muka fara soyayya, sai dai asibitoci ba sa gwajin cutar MG idan alamominta ba su bayyana ba."

"Bayan wata guda sai na fara jin wasu alamomi - matsanancin ciwo idan ina fitsari da kuma fitar wani miki a mafitsarata - sai dai ban san abin da da ke faruwa ba."

"Bayan wasu 'yan makonni sai ta bayyana cewa ina dauke da kwayar cutar, amma budurwata lafiyarta kalau, kuma wannan bai yi ma'ana ba. Sai dai aka sake yi mata wani gwaji, inda a nan ne aka gano cewa tana dauke da kwayar cutar."

"An ba mu maganin da muka rika sha har na tsawon makonin biyu, amma mun yi kwanaki biyar ba mu sadu da juna ba domin mu tabbatar mun warke."

Ya ci gaba da cewa: "Bayan karin wasu gwaje-gwaje sai muka gano cewa ba ta dauke da kwayar cutar."

"Sai dai duk da haka miki ya rika fita daga mazakutata, amma an fada mini cewa zai tafi. Daga bisani ya tsaya."

"Na kamu da cutar mafitsara kuma alamomin cutar iri daya ce da cutar MG. "

"A yanzu ina da tabbacin cewa cutar ce ta dawo kuma ina jiran sakamakon karin gwaje-gwajen dana yi."

"Sai dai asibiti kula da masu ciwon sanyi sun ki su yi wa budurwata gwaji saboda ba ta nuna alamomi ba."

"Ina ganin ya kamata asibitoci su rika gwajin cutar MG a matsayin daya daga cikin ciwon sanyi saboda tun farko da an gano ina dauke da cutar."

'Ba ta jin magani'

Hukumar kiwon lafiya ta Ingila ta ce an fara gwaji a kan cutar MG kuma za a taimaka wa duk wani da ya sha magani da bai warke ba, idan bukatar yin haka ta taso.

Dokta Helen Fifer, kwararriyar likita ce kan kwayoyin da ke haddasa cututtuka a hukumar lafiya ta kasar, ta yi maraba da ka'idojin kuma ta kara da cewa :

"Idan ka nuna alamun ciwon sanyi za mu baka shawarar yin gwaji a asibiti kula da ciwon sanyi da ke kusa da kai."

"Kowa zai iya kare kansa daga ciwon sanyi ta hanyar amfani da kororon roba tare da mutanen da ba koyaushe suke saduwa da su ba."