Kun san yadda za ku magance warin jiki?

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Baya ga hasken rana da ake samu a lokacin zafi, yanayin ya kan kuma zo da wasu abubuwa da mutane ba sa maraba da su kamar sanya warin jiki.

A yanzu masu ilimin kimiyya na Jami'ar York da Oxford na Ingila sun ce sun nemo tabbacin abun da ke kawo warin jiki wanda ke fita ta tsattsafin zufa wanda wasu kwayoyi ke kawo wa.