Ronaldo na bacci zai rika karbar miliyan 12 a Juve

Cristiano Ronaldo
Bayanan hoto,

Duk minti daya Ronaldo zai karbi sama da naira dubu 24

Yawan kudaden albashin da Cristiano Ronaldo zai karba a Juventus na ci gaba da jan hankali duk da yana dab da cika shekara 34.

Juventus ta sayo Ronaldo kan kudi fan miliyan 99.2, inda gwarzon dan wasan na duniya ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara hudu.

Hakan na nufin duk shekara Ronaldo zai karbi kusan fan miliyan 26 a shekaru hudu na yarjejeniyarsa a Juventus, wato sama naira biliyan 12.

Ba kananan kudade ba ne Ronaldo zai karba idan aka lissafa yawan adadin a rana zuwa mako har zuwa wata, da ma lokacin da dan kwallon yake bacci.

Wannan ne ma ya sa ma'aikatan kamfanin Fiat, wanda shi da Juventus duka mallakin ilayan Allegri ne, suka yi zanga-zanga domin nuna adawa da yawan kudaden.

Yana bacci yana karbar miliyan 12

A rana Ronaldo zai karbi kusan fan 73,000, kwatankwacin naira kusan miliyan 36.

Ronaldo wanda ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Real Madrid, yana cikin 'yan wasa hudu da suka fi kowa tsada a duniya.

Yana bayan Neymar da Mbappe na PSG da kuma Coutinho na Barcelona.

A mako Ronaldo zai karbi sama da fan miliyan £510,483 wato sama da naira miliyan 258.

Duk awa daya zai karbi fan 3,038 wato kusan naira miliyan daya da rabi, yayin da a duk minti daya zai karbi £50.64 wato sama da naira dubu 24.

Hakan na nufin kimanin awanni takwas da Ronaldo zai shafe yana bacci a dare zai karbi sama da fan 24,000 kwatankwacin sama da naira miliyan 12.

Albashin Ronaldo a Juventus

Naira biliyan 50 aka sayo shi

N12.5b

A shekara

Naira 1b

A duk wata

 • N258m A duk mako

 • N36m A duk rana

 • N1.5m A duk awa daya

 • N12m A awanni takwas na baccinsa

Getty

'Real Madrid ta sauya rayuwata' - wasikar Ronaldo ga magoya bayan Madrid

Shekarun da na shafe a Real Madrid da wannan birnin, kusan su ne mafiya dadi a rayuwata.

Ina matukar nuna jin dadi da godiya ga wannan kulob da magoya bayansa da kuma birnin Madrid.

Babu abin da zan iya yi sai dai nuna godiya ga wannan kulob, da magoya baya da kuma birnin. Ina mika godiya ta kan soyayya da kaunar da aka nuna min.

Sai dai, na yi amannar cewa lokaci ya yi da zan bude wani sabon shafi a rayuwata, a don haka na nemi kulob din ya sayar da ni.

Haka na ke ji, kuma ina neman kowa, musamman magoya bayanmu, su fahimci inda na sa gaba da kuma matakin da na dauka.

Hakika sun yi duk abin da ya kamata a shekara tara da ta gabata. Shekaru ne da babu kamarsu.

Lokaci ne na nuna dattaku da jimami, na yi dogon tunani, sai dai abu ne mai tsauri saboda Real Madrid na sahun gaba.

Sai dai na sani hakika ba zan taba mantawa da irin kwallon da na taka a nan ba, da kuma irin nasarorin da na samu.

Na zauna da abokan wasa masu kirki matuka, kuma mun yi rayuwa mai dadi.

Magoya baya sun nuna mana kauna kuma tare mun lashe kofin zakarun Turai uku a jere - biyar a shekara hudu.

Kuma na lashe lambobin yabo a karon-kaina. Na lashe kyautar Kwallon Zinare hudu da Takalmin Zinare uku. Duka a wannan gagarumin kulob.

Real Madrid ta sauya rayuwata, da ta iyali na, a don haka ne nake mika godiya ta: Ina godewa kulob din, da shugabansa, da daraktoci, da abokan wasa na, da likitoci, da jami'an lafiya da kuma ma'aikatan da suka taimaka mana.

Ina sake mika godiya ga magoya baya da jami'an kwallon kafa na Spain.

A shekaru taran da na shafe a nan, na murza-leda da gogaggun 'yan wasa. Ina martaba dukkanninsu.

Na yi doguwar shawara kafin daukar wannan mataki, zan bar Real Madrid, zan daina sanya rigarta, zan bar filin wasa na Santiago Bernabéu, amma za ta ci gaba da kasance wa a zuciyata a duk inda nake a duniya.

Ina godewa kowa-da-kowa, kamar yadda na fada a karon farko a filin wasanmu shekara tara da ta gabata: A ci gaba da gashi Madrid.

Bajintar Ronaldo

Bayanan hoto,

Sau biyar Cristiano Ronaldo yana lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or

 • Ronaldo ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Madrid
 • Ya ci kwallaye 105 a gasar Zakarun Turai
 • Kwallaye 311 a gasar La Liga
 • Kofi 16 a Real Madrid da suka hada da La liga biyu da Zakarun Turai hudu da gasar duniya ta kungiyoyi
 • Ya ci kwallaye uku-uku (hat-tricks) shi kadai sau 44, kuma sau 34 a La Liga
 • Sau takwas yana cin kwallaye fiye da hudu a Real Madrid
 • Ya taba cin kwallaye 61 a kakar 2015-16 a dukkanin wasanin da ya buga
 • Hakan ya hada da kwallaye 48 a La Liga
 • Kwallaye 659 ya ci a rayuwarsa - biyar a Sporting Lisbon, da 118 a Manchester United da 451 a Real Madrid da 85 a Portugal
 • Sau biyar yana lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or