Rasha 2018: 'Yan Kenya na fushi da 'yan majalisarsu

Millicent Omanga tare da magoy abayan kasar Kuroshiya Hakkin mallakar hoto Millicent Omanga
Image caption Sanata Millicent Omanga ta halarci wasan Kuroshiya da Ingila na kusa da na karshe

'Yan Kenya sun nuna fushinsu da yadda wasu 'yan majalisa su 20 suka tafi kallon gasar kwallon kafa ta duniya a Rasha da kudin kasa.

'yan majalisar za su shafe mako biyu suka kallon wasanni hudu da suka hada da wasan karshe, tafiyar da aka ce za ta janyo ma kasar asarar dubban dalolin Amurka.

Hankalin 'yan kasar ya tashi ne bayan da wasu 'yan majalisar suka raba hotunan da suka dauka a yayin da suke cikin filayen wasannin.

Ministan Wasanni Rashid Echesa ya fada ma BBC cewa ya amince da tafiyar 'yan majalisa shida ne kawai domin suyi nazarin yadda ake shirya irin wannan gagarumar gasar.

Kasar ta Kenya dai ba ta taba samun gurbin shiga gasar ta kwallon kafa ta duniya ba, kuma a halin yanzu su ne ke matsayin na 112 cikin kasashe 2016 a jadawalin FIFA na kasashen duniya.

Amma kasar na cikin manyan kasashen da suka yi fice wajen wasannin tsalle-tsalle da guje-guje.

Amma yawancin 'yan kasar na kallon wannan tafiyar a matsayin almubazzaranci, a kasar da dan kasa baya samun fiye da dalar Amurka 150 (wato Naira 54,000) a wata.

Akwai rahotanni da ke cewa 'yan majalisar na karbar kimanin dala 1,000 ne a kowace rana.

Karin bayani