Nawaz Sharif zai koma Pakistan duk da za a kama shi

Supporters were outraged when Nawaz Sharif was handed a 10-year jail sentence last week Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Magoya bayan Nawaz Sharif sun fusata bayan da aka yanke masa hukuncin daurin shekara 10 a makon jiya

Korarren Firayi ministan Pakistan Nawaz Sharif na kan hanyar komawa gida duk da ya san za a kama shi ne da ya isa kasar.

Mista Sharif na fuskantar daurin shekara 10 a kurkuku saboda laifukan cin hanci da rashawa.

'Yar Mista Sharif din Maryam Sharif ma na fuskantar dauri da zarar sun isa Lahore daga Landan a yau Juma'a.

Ya ce "Duk da cewa na san babu makawa sai an daure ni, amma ba zan fasa komawa Pakistan ba."

A wancan karon da aka taba yanke ma Nawaz Sharif hukuncin dauri a kurkuku, ya zabi ya bar kasar bayan da Saudiyya ta shiga tsakani.

Wannan lamarin ya auku ne a shekarar 1999 bayan da sojin Pakistan suka hambarar da gwamnati mai ci a lokacin.

Amma a wannan karon, ya zabi ya tafi kurkuku duk da cewa yana kasar Ingila ne a halin yanzu.

A wancan zamanin, an dauka cewa ba zai iya jure ma zaman gidan kaso ba ne saboda shagwababbe ne dan wani attajiri.

Hakkin mallakar hoto MARYAM SHARIF
Image caption An ce Maryam Sharif ce ta fi kowa iko a lokacin Mista Sharif na kan mulki

Amma da alama matakan da yake dauka yanzu sun tabbatar da cewa a shirye yake ya fuskanci dukkan gwagwarmayar da siyasar kasar ta zaba masa.

Kana Sharif ya san cewa za a sami tirjiyar siyasa bayan babban zaben da ke tafe, lamarin da magoya bayansa ke kallo a matsayin wata makarkashiyar siyasa domin kayar da jam'iyyarsa ta PML-N a zaben.

Ya kuma sani sarai cewa wannan matakin na tattare da mummunan tasiri a gre shi, domin zai tafi ya bar matarsa Khulsoom a asibiti, inda ta ke jinyar cutar daji, kuma likitoci na ganin ba ta da sauran lokaci mai yawa kafin rai yayi halinsa.

Labarai masu alaka