Ana zargin fasto da yi wa wata mata fyade

Wasu dalibai a Indiya na zanga zangar nuna adawa da fyaden da aka yi wata yarinya mai shekara 8 a Kashmir.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana sa ran wasu limaman coci biyu da ake zargi za su mika wuya

Daya daga cikin fada-fada hudu da ake tuhuma da yi wa wata mata fyade a jihar Kerala da ke Indiya ya mika kansa ga jami'an 'yan sanda.

Kotu a Kerala ta ki ba da belinsa da kuma wasu limaman coci su biyu, wadanda ake sa ran za su mika kansu.

Matar mai shekara 34, ta yi zargin cewa an yi mata fyade bayan an yi barazanar ba ta sunanta domin ta yarda a yi lalata da ita.

Har yanzu 'yan sanda ba su cafke fada na hudu ba.

Tuhumar ta fito fili ne a watan Fabrairun da ya gabata lokacin da mijinta ya gano ana yi wa matar tasa barazana.

A ranar 2 ga watan Yuni ne aka shigar da koke a gaban hukumar 'yan sanda bayan da wata tattaunawa da aka nada da aka yi tsakanin mijinta da kuma wani jami'in coci ya bayyana a kafofin sada zumunta.

"Ba da kai ga mace ta hanyar amfani da barazana fyade ne," kamar yadda wani jami'in 'yan sanda ya shaidawa sashen Hindi na BBC."

Ya kara da cewa mijin matar ya yi wa jami'an coci korafi a watan Mayun da ya gabata amma ba su dauki mataki cikin gaggawa ba.

An dai dakatar da limaman coci su hudu daga ayyukansu na yau da kulum tun bayan faruwar al'amarin.

Kakakin cocin Malankara ya shaidawa BBC cewa an fara gudanar da bincike a cikin cocin.

A cikin koken da aka shigar gaban hukumar 'yan sanda, daya daga cikin limamen cocin ya fara cin zarafin matar ne ta hanyar yin lalata da ita lokacin da take da shekara 16.

Bayan ta fadawa wani limamen cocin abin da ke faruwa da ita, sai shi ma ya nemi yin lalata da ita ta hanyar yin bazarar bata sunanta idan ba ta amince ma shi ba.

Matar ta kuma ce wasu limamen cocin biyu sun yi mata fyade lokacin da ta je wurinsu domin su taimake ta.

Ta ce sun yi barazanar tozarta ta a gaban jama'a idan ba ta amince sun yi lalata da ita ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kashi 20 cikin dari na yawan alummar jihar Kerala kiristoci ne

Zargin ya gigita al'ummar cocin ta Malankara da ake kira Orthodox Syrian Church wacce ke tasiri a Kerala, inda kashi daya bisa biyar na yawan al'ummar jihar magoya bayan cocin ne.

"Babu wata kididdiga a kan yadda girman matsalar cin zarafin mata ta hanyar lalata da su ta ke a cikin coci duk da cewa kowa ya san da matsalar. Amma babu wanda ya ke magana ". In ji Kochurani Abraham, mai fafitukar kare hakkin mata a coci.