An ci tarar Johnson & Johnson biliyoyin daloli kan hodar yara

Hodar jarirai ta Johnson & Johnson

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Johnson & Johnson ya ce binciken kimiya ya nuna cewa hodarsa ba ta da illa

Kotu ta umarci Kamfanin kamfanin Johnson & Johnson ya biya diyyar kudi fiye da dala biliyan 4 ga wasu mata su 22 wadanda suka yi zargin cewa hodarsa ta sa sun kamu da cutar Sankarar jakar kwai (ovarian cancer).

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci a jihar Missouri da ke Amurka da farko sun sa kamfanin ya biya matan diyyar dala miliyan 550 kuma daga bisani su kara dala biliyan 4.1 domin ya zame masa izina.

Hukuncin na zuwa ne a lokacin da katafaren kamfanin maganin ya ke gwagwarmaya da wasu a gaban kotu kan hodar jariransa.

Sai dai J&J ya ce "ya ji takaici sosai" kuma zai daukaka kara.

A shari'ar da aka yi cikin makonni shida, matan da iyalansu sun ce sun kamu da cutar sankarar jakar kwai bayan da suka yi shekara da shekaru suna amfani da hodar jarirai na kamfanin.

Shida daga cikin mata 22 da suka shigar da kara a gaban kotu sun mutu sakamakon kamuwa da cutar sankarar jakar kwai.

Lauyoyinsu sun yi zargin cewa akwai sinadarin asbestos mai guba a cikin hodar tun daga shekarun 1970 sai dai sun gaza wajen yi wa kwastamominsu gargadi kan hadarin da ke ciki.

'Ba bu adalci a cikin hukuncin'

Farin kasa da ake amfani da shi wajan yin hodar wani abu wanda a wasu lokutan ana samunsa a cikin kasa kusa da sinadarin asbestos.

J&J ya musanta zargin da ake yi cewa akwai sinadarin asbestos a cikin kayayakinsa kuma ya nanata cewa ba sa janyo cutar sankara .

Katafaren kamfanin ya kuma kara da cewa an yi bincike da dama kuma duk sun nuna cewa hodarsa ba ta da wata illa kuma "ba a yi masa adalci ba" a hukuncin da kotu ta yanke.

Hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta Amurka (FDA) ta yi bincike kan samfurin hoda daban daban ciki har da na kamfanin J&J, daga shekarar 2009 zuwa 2010. Bata gano sinadarin asbestos a cikin dukaninsu ba.

Masu shigar da kara sun fada wa kotun da ke Missouri cewa hukumar ta FDA da kamfanin Johnson & Johnson sun yi amfani da matakan da basu da ce ba a gwajin da suka yi.

Shin ko sinadarin talc ba shi da illa?

An dade ana nuna damuwa kan yadda ake amfani da hodar musaman a al'aurar mata , kan iya jefa rayuwarsu cikin hadarin kamuwa da sankarar jakar kwai sai dai ba a cimma matsaya ba kan shaidar da ake da ita. Hukumar bincike kan cutar sankara ta ce hodar da ake amfani da ita a al'aura kan iya kawo cutar sankara

Shin me yasa ake mahawara?

Farin kasa da ake amfani da shi ba shi da sinadarin asbestos kuma ba ya janyo sankara, sai dai tun shekarun 1970 ake amfani da farin kasa a cikin hodar jarirai da kuma sauran kayan kwalliyar mata.

Sai dai bincike da aka yi kan farin kasa da ba shi da sinadarin asbestos ya ba da sakamako masu karo da juna.

Wasu bincike sun ce akwai hadarin kamuwa da cutar sai dai wasu sun nuna damuwa kan cewa babu adalci a cikin bincike saboda a mafi yawan lokuta binciken ya dogara ne kan yadda mutane suka tuna da irin yawan hodar da suka yi amfani da ita a shekarun baya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hodar da ake kadamma a kanta

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai wasu bincike sun ce sam babu wata alaka tsakanin cutar sankara da hoda kuma babu wata alaka tsakanin hoda da abubuwan da ake amfani da su domin kayyade haihuwa irinsu kororon roba da kuma robar da ake saka mata a cikin mahaifa (wadanda suke kusa da jakar kwai) da sankara.

Haka kuma babu wata shaida da ta nuna cewa yawan hodar da aka amfani da ita kan iya kawo cutar sankara kamar yadda ake gargadi kan yawan shan taba na kawo sankarar huhu .

Shin me ya kamata mata su yi?

Kungiyar agaji ta Overcome ta ce akwai rauni a shaidar da aka gabatar kuma hodar na kara jefa rayuwar mata cikin hadarin kamuwa da cutar sankarar jakar kwai, bincike ya nuna cewa kusan kashi daya bisa uku na mata ne zai shafa . Ta ce hadarin ba sosai ba ne saboda sankarar jakar kwai cuta ce da ba kasafai ake kamuwa da ita ba .

Akwai wasu abubuwa da ke kawo sankarar jakar kwai ciki har da gado da muhali, ba wai hoda kadai ba.

Kungiyar ta kara cewa: "ko da hoda tana kara yiwar kamuwa da cutar sankara, mata kalilan ne masu amfani da hoda za su kamu da cutar sankarar jakar kwai .Kuma idan wata tana fama da cutar sankarar kwai ba za a iya cewa hoda ce ta sa ta kamu da cutar ba."

Hukunci mai cike tarihi

Wannan shi ne hukuncin da ya sa kamfanin J&J ya biya makudan kudi a duk tuhumar da ake yi masa.

Sai dai wasu alkalai ko kotun daukaka kara kan rage yawan kudin da aka ce ya biya a matsayin diyya kuma a baya kamfanin J&J ya yi nasara wajan ganin shariah ta yi watsi da wasu hukunce hukunce da masu taimaka wa alkali suka yanke

Wani hukunci da aka yanke a shekarar 2017 a California ya nemi a biya wata mata diyyar dala miliyan 417 wadda ta ce ta kamu da cutar sankarar jakar kwai bayan ta yi amfani da kayan kamfanin, ciki har da hodar jarirai.

Sai dai daga bisani wani alkali ya yi watsi da hukunci kuma har yanzu akwai kararraki a gaban kotu da ba a yanke wa hukunci ba da ya shafi kamfani.

Akasarin matan su 22 na zaune ne a wajen jihar Missouri

Johnson & Johnson ya ce : "Duk hukuncinda aka yanke kan J & J a cikin kotun nan mun daukaka kara akansa inda kotu ta yi watsi da shi kuma kura kuran da ke cikin wannan shariar ya fi hukuncin da aka yi a baya wanda kotu ta yi watsi da shi ."