Giwaye sun kashe mutane a Bauchi

Giwaye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnatin Bauchi ta jajantawa iyalan wadanda al'amarin ya shafa

Giwaye a gandun dajin Yankari sun kashe mutane biyu a yayin da suke kokarin taba su da kuma daukar hoto.

Rahotanni sun ce wani yaro dan shekara tara da kuma wani tsoho mai shekara 45 ne suka gamu da ajalinsu a kauyen Bajama da ke kusa da gandun dajin.

Shugaban gandun dajin Habu Mamman wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, ya ce a ranar 8 ga watan Yuli ne giwayen suka fita da safe inda suka ratsa ta Sharam zuwa Bajama.

"Bayan giwayen sun shiga dajin Gwartanbali ne sai mutanen kauyen da dama suka kewaye giwayen suna daukarsu hoto tare da kokarin taba su." in ji shi.

Ya ce wannan ne dalilin da ya sa giwayen suka harzuka suka tarwatsa gangamin mutanen, kuma a yayin da kauyawan ke gudu ne giwa ta take yaro dan shekara tara bayan ya fadi, kuma a nan take ne ya mutu."

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar ya jajantawa iyalin wadanda al'amarin ya shafa.

Ya kuma yi kira ga jama'a game da hatsarin da ke tattare da kusanci da dabbobin gandun dajin na Yakari, inda ya ce daga nesa ya kamata a dinga kallonsu.

An dauki lokaci kafin masu kula da gandun dajin suka kora giwayen da kuma kokarin korar mutanen kauyen da ke bin giwayen.

Hukumomin gandun dajin sun ce wannan ba sabon abu ne da giwaye ke haduwa da mutanen kauye da ke kusa da gandun dajin Yankari amma sun bayyana cewa wannan ne karo na farko da irin wannan al'amari ya faru a gandun dajin.