Shugaban Kamaru Paul Biya zai tsaya takara karo na bakwai

Paul Biya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Paul Biya yana yawan tafiya kasashen waje domin duba lafiyarsa

Shugaban Kamaru Paul Biya ya ce zai sake neman shugabancin a babban zaben kasar wanda za a yi a watan Oktoba.

Mista Biya wanda ya shafe fiye da shekara 35 yana mulkin kasar ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter a ranar Juma'a.

Shugaban mai shekara 85 ya haye karagar mulki ne a shekarar 1982 kuma yana daya daga cikin shugabannin nahiyar Afirka wadanda suka dade a kan mulki.

Ya ce: "Ina so don kashin kaina na amsa kiraye-kirayen da dimbin jama'a suke yi min. Na amince zan tsaya a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter cikin harshen Faransanci da kuma Turancin Ingilishi.

A karkashin mulkin shugaban, Kamaru ta fita daga matsin tattalin arziki da kuma sauya tsari bin jam'iyya daya tilo, inda kasar ta rungumi tsarin jam'iyyu daban-daban.

Sai dai da kuma ta fuskanci matsalolin cin hanci da rashawa da kuma koma baya ta fuskar bin tafarki dimokradiyya.

Hakan ne ya kai ga dakatar da kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa a shekarar 2008.

A 'yan shekarun nan kasar ta yi fama da barazanar ballewar yankin da ke magana da Turancin Ingilishi, inda ake cigaba da samun tashin hankali tsakanin 'yan aware da kuma dakarun gwamnati.

Shugaba Paul Biya yana yawan tafiya kasashen waje domin duba lafiyarsa, abin da ya sa wasu ke nuna damuwa kan ko zai iya cigaba da jan ragamar kasar kamar yadda ya kamata.