Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Wasu daga cikin hotunan 'yan Afirka daga sassan duniya da nahiyarna wannan makon.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata zabiya mai tallan kayan kawa a bikin da aka yi a Afirka ta kudu a ranar juma'a a Durban a watan Yuli wanda ya hada da tsere in da masu ado ke nuna adon su.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kiristoci na kasar Masar Tawadros II, tare da shugaban cocin Katolika Paparoma Francis sun saki kurciya bayan taron da suka yi a Italiya.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu doki na wasan sukuwa a ranar bude bukin Berber a kasar Morocco
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron shekara-shekara a garin Tan-tan na hamadar yamma don raya al'adunsu ...
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption kuma yana janyo makiyaya daga duk fadin gabancin Afirka.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani dan wasan zari ruga na Uganda Cranes' Michel Okorach ya kare dan wasan Kenya Vincent Mose a lokacin gasa a Nairobi, babban birnin kasar Kenya ranar Asabar.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hoton 'yan makaranta a layin abincin a ranar Laraba a Kajiado kudancin Kenya.
Hakkin mallakar hoto GHIDEON MUSA ARON VISAFRIC/Reuters
Image caption Rugumar da ta shiga tarihi a tsakanin firay ministan Ethiopia da takwaransa na Eritrea inda suka kawo karshen yakin tsawon shekaru 20 a tsakaninsu
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya gaishe da shugaba Muhammadu Buhari a birnin tarayya Abuja ranar Laraba 11 ga watan Yuli.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar kwallon kafa ta nakkasassu ta Najeriya ta hadu don yin addu'a kafin fara horo a birnin Legas ranar Jumma'a.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan jarida na Uganda a wurin zanga-zanga inda 'yan sanda suka saka harba hayakin da ke sa kwalla don korar masu zanga-zanga a Kampala ranar Laraba...
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lokacin da yara ke kallon wasan kwaykwayyo na yara a lokacin da aka je hutu a gasar kwallon kafar duniya tsakanin Brazil da Belgium a gabashin Mozambique.

Labarai masu alaka

Labaran BBC