Zaben Pakistan: Fiye da mutum 100 sun rasa rayukansu a harin bam

A man who was injured in a suicide bomb attack that targeted an election campaign rally of the Balochistan Awami Party (BAP), talks on a mobile phone, in Mastung, Pakistan, 13 July 2018.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wannan ne hari mafi muni da aka kai a Pakistan tun shekarar 2014

Wani dan kunar bakin wake ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 128 a lokacin wani gangamin zabe a kudu maso yammacin Pakistan.

Wannan ne hari mafi muni da aka kai a Pakistan tun shekarar 2014.

A cikin wadanda suka mutu akwai wani dan takara daga garin Mastung, kamar yadda jami'an 'yan sanda suka sanar. Kungiyar IS ce ta dauki alhakin kai harin.

Tun da farko, wani harin na daban da aka kai a garin Bannu ya janyo mutuwar mutum hudu.

Hare-haren sun auku ne gabanin zaben kasa da za a yi ranar 25 ga watan Yuli.

A wannan ranar ce aka kama tsohon firai minista Nawaz Sharif bayan da ya koma gida daga Ingila.

Hukumar NAB ce ta damke shi tare da 'yar sa Maryam bayan sun sauka a birnin Lahore da ke arewacin kasar. Daga baya an wuce da su wani gidan kurkuku a babban birnin kasar Islamabad.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An kama Nawaz Sharif bayan komawarsa gida daga Birtaniya