Aljeriya ta 'daina cin zarafin 'yan ci-rani a Sahara'

A migrant from Niger hides with her newborn child to avoid deportation at a transit centre in Tamanrasset in southern Algeria, 2 July 2018

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan ci-rani daga Afirka kimanin 100,000 ne suka nemi isa Turai ta cikin Aljeriya

Wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan 'yan ci-ranin da ke keta hamadar Sahara a kafa ta cikin Aljeriya sun ragu matuka.

Hukumar da ke kula da 'yan ci-rani a duniya wato International Organization for Migration take hidima kan kimanin mutum 10,000 da aka yi watsi da su a iyakar Aljeriya da ke kudancin kasar.

Wasunsu masu fasakwaurin mutane ne suka gudu suka barsu, amma wasu kuwa hukumomin Aljeriya ne suka kore su, inji hukumar ta IOM.

Amma gwamnatin Aljeriya ta musanta wannan tuhumar da ake mata.

A halin yanzu ana iya cewa 'yan ci-rani sun kusa daina bin hanyar gaba daya saboda hatsarin da ke tattare da yankin.