Rikicin Kamaru: Ministan tsaro ya tsallake rijiya da baya

Paul Biya na Kamaru

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Paul Biya na Kamaru

Gidan rediyon gwamnatin Kamaru ya ce 'yan aware na kasar sun kai wani hari kan ayarin motocin ministan tsaron Kamaru Joseph Beti Assomo.

An kai ma ministan tsaron hari ne a cikin yanki mai amfani da harshen Ingilishi da ke kudu maso yammacin kasar.

Gidan rediyon ya kuma ce an yi nasarar kashe wasu daga cikin maharan - wadanda ake kyautata zaton 'yan tawaye.

Sojojin kasar hudu da wani dan jarida na cikin wadanda suka sami rauni.

An dai shafe watanni ana kai ruwa rana tsakanin gwamnatin kasar da 'yan aware da suke son kafa kasarsu mai suna Ambazoniya.

Sun ce masu amfani da harshen faransanci na danne su.

Labarin wannan harin ya fito ne a daidai lokacin da shugaban kasar Paul Biya mai shekaru 85 ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na bakwai.