An bude rumfunan zabe a jihar Ekiti

An tura jami'an tsaro na Najeriya kimanin 30,000 zuwa jihar ta Ekiti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An tura jami'an tsaro na Najeriya kimanin 30,000 zuwa jihar ta Ekiti

A Nigeria an bude runfunan zabe a jihar Ekiti, dan zabar sabon gwamna da zai mulki jihar na tsahon shekara hudu masu zuwa.

Kafin zuwan wannan rana dai an yi ta samun korafe-korafe daga jam'iyyun adawa musamman PDP da APC.

Gwamnatin Najeriya ta jibge jami'an tsaro a jihar dan tabbatar da tsaro a lokacin zaben, wanda hakan ya sanya 'yan adawa zargin ana son musguna musu ne yayin zaben.

Wakilin BBC Umar Shehu Elleman da ke jihar ya rawaito cewa babu alamun tashin hankali tsakanin al'umar jihar duk da banbancin goyon bayan jam'iyyun siyasa.

Wasu daga cikin 'yan jihar da ya zanta da su sun bayyana irin shirin da suka yi don zuwa rumfunan zabe.

Yayin da wasu suka nuna gamsuwa kan matakan tsaron da aka dauka, domin gujewa tashin hankali a lokacin wannan zabe mai muhimmanci.

Ana iya tunawa da yadda aka gudanar da irin wannan a zabukan a baya, inda aka rika samun tashin hankali da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin miliyoyin Naira.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da shirin da ta yi domin raba kayan zaben a kan lokaci da kuma bude rumfunan zaben a fadin jihar.

A bangare guda kuma masu sanya ido kan zaben sun shirya tsaf dan fara aikin da ya rataya a kansu, wanda ake sa ran za su gabatar da rahoton abin da ya faru a lokaci da bayan zabe.

Fafatawar dai za ta fi zafi tsakanin dan takarar gwamna na jam'iyyar APC mai mulki da na jam'iyyar PDP, babbar jam'iyyar adawa a kasar wadda ita ce ke mulkin jihar a yanzu.