'Ana kai hare-hare kauyukan Adamawa'

Bindow Hakkin mallakar hoto BINDOW TWITTER
Image caption Gwamnatin jihar Adamawa na ganin hare-haren na da alaka da masu tayar da kayar baya

Gwamnatin jihar Adawama ta ce ana samun hare-haren 'kan-mai-uwa-da-wabi' a kauyukan wasu kanan hukumomin jihar dake arewa maso gabashin Najeriya.

Kwamishinan yada labaran jihar ta Adamawa, Ahmed Sajo, ya shaida wa BBC cewar, hare-haren da aka fara kai wa cikin kwanaki ukun da suka gabata sun shafi kimanin kanan hukumomin shida.

A wata zantawar da ya yi da wakilinmu, Sajo ya ce kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da Girei da Demsa da Numan da Shelleng da Guyuk da kuma Mayo-Belwa.

Wannan na zuwa ne a lokacin da wasu kafafan watsa labarai a Najeriyar ke cewa an far ma wasu kauyukan Fulani a yankin.

Sajo ya ce a ranar farko ne dai aka samu rahoton cewar maharan sun kashe mutane.

Bayan haka dai maharan lalata kauyuka da gonaki suke yi, inji kwamishinan, yana mai cewa wannan ya sa gwamnati ta fara tunanin hare-haren na masu tayar da kayar baya ne maimakon na kabilanci.

Kwamishinan dai ya ce gwamantin ta tura jami'an tsaro yankin domin dakile hare-haren.

Sajo ya ce gwamnatin tana kokarin hada kan al'ummomin jihar domin rashin hadin kai ne zai sa baki su rinka kai wa al'ummomin jihar hare-hare.

Kawo yanzu dai gwamnatin jihar ba ta tantance adadin mutanen da lamarin ya shafa ba ko kuma dukiyar da aka lalata a hare-haren

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An tura jami'an tsaro yankin domin dakile hare-haren

Jihar Adamawa na dai daya ce daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Labarai masu alaka