An kama mace don ta rungumi mawaki

Mawaki Majid al-Mohandis Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY IMAGES

An kama wata mata a kasar Saudiyya bayan ta ruga da gudu kan dandamali ta rungumi wani mawaki a yayin wani taron wake-wake.

Matar ta rungumi mawakin mai suna Majid al-Mohandis, a lokacin da ya ke rera waka a taron wake-waken da aka yi a yammacin birnin Taif.

Hotunan bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna matar ta kankame mawakin, yayin da jami'an tsaro kuma ke kokarin cire ta daga jikinsa.

Ba a amince wa mata su rinka cakuduwa da mazan da ba muharramansu ba a kasar ta Saudiyya.

Mawakin wanda dan asalin kasar Iraqi ne, amma yana da shaidar zama dan kasa a Saudiyya, ya shahara wajen rera wakokin a kasar, kuma har yanzu bai ce komai ba a kan lamarin.

Bayan faruwar lamarin, Majid al-Mohandis, bai tsaya ba ya ci gaba da wakarsa.

Yanzu dai mai shigar da kara na gwamnati zai duba yi wuwar tuhumar matar da laifukan da suka shafi musgunawa.

Matar wadda ba a bayyana sunanta ba dai na sanye ne da nikabinta inda ta rufe jikinta ruf ba a ganin komai sai idanuwanta.

Kasar Saudiyya dai na da tsauraran dokoki na tabbatar da kyawawan dabi'u da haramcin shan barasa da hana sa tufafi masu nuna tsiraici da kuma nuna wariyar jinsi.

A shekarar da ta gabata ne yariman kasar Mohammed bin Salman, ya sassauta dokar da aka dade ana amfani da ita wadda ta haramta wa mata halartar wuraren tarurruka na al'umma.

Karanta wasu karin labaran

Labarai masu alaka