APC ta lashe zaben Ekiti

Ana gudanar da zabe a jihar Ekiti

Hukumar zaben Najeriya (INEC) ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar inda jam'iyyar APC ta yi nasara.

Jam'iyyar ta APC ta samu yawan kuri'un da ya kai 197,459, yayin da jam'iyya mai mulki a jihar wato PDP ta samu kuri'u 178,121.

Hakan ya nuna cewa Dr. Kayode Fayemi, na jam'iyyar APC shi ne ya lashe zaben.

Jam'iyyu 35 ne suka fafata a zaben to amma karawar ta fi zafi a tsakanin jam'iyyar PDP mai mulki da kuma jam'iyyar adawa ta APC a jihar.

Tuni dai magoya bayan jam'iyyar APC suka fantsama kan tituna a sassan jihar domin nuna farin cikinsu a kan nasarar da jam'iyyarsu ta samu.

A ranar Juma'ar da ta wuce ne dai rahotanni suka ce duk jam'iyyun na bayar da kudi ga masu zabe a zaben da ake yi ranar Asabar.

A wani labarin kuma, hukumar kula da harkokin kafofin watsa labarai ta Najeriya, ta bayar da umarnin rufe gidan rediyon jihar Ekiti sakamakon yadda ya fara bayar da sanarwar sakamakon zaben tun kafin hukumar zabe ta bayar.

Asalin hoton, FaceBook/Kayode Fayemi

Bayanan hoto,

Kayode Fayemi ya zama gwamnan Ekiti mai jiran gado bayan hukumar INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben jihar

Hukumar kula da kafofin watsa labaran ta ce gidan rediyon zai ci gaba da zama a rufe har sai abin da hali ya yi.