Minista ya yi murabus saboda aika sakon batsa ga mata

Andrew Griffiths Hakkin mallakar hoto UK Parliament

Ministan kananan ma'aikatun Birtaniya, Andrew Griffiths, ya ajiye mukaminsa bayan ya tura wasu sakonnin tes na batsa ga mata biyu a mazabarsa.

Jaridar Sunday Mirror ce ta bayyana abin da sakonnin suka kunsa.

Mista Griffiths, dan wajalisa mai wakiltar Burton, wanda kuma ya kasance shugaban ma'aikatan Theresa May a lokacin da take adawa tsakanin shekara 2004 zuwa 2006, ya shaida wa Mirror cewar "ya ji matukar kunya".

Ya ce abin da ya yi saka matarsa da iyalinsa "a wani mawuyacin hali".

Mista Griffiths ya kuma nemi gafara game da "tsabar kunyar" da ya janyo wa Firayim minista da kuma gwamnatin kasar, a cikin wata sanarwar da ya fitar wa jaridar.

Dan majalisan ya kasance yana bin matan a shafin Snapchat na tsawon wata shida kafin ya tura musu sako a watn Yuni.

Imogen Treharne,mai shekara 28, ta shaida wa Mirror cewar sakonnin sun fara zuwa ne da yammacin wata rana bayan ta wallafa wani bidiyo mai "jan hankali".

Mista Griffiths ya shaida wa matar da ke aiki a gidan sayar da barasa cewar ya yi imanin cewar an wallafa bidiyon ne domin shi ya yi tsokaci, in ji Mis Treharne .

Ta shafukan Facebook da Instagram da WhatsApp da kuma Snapchat, rahotanni sun ce Mista Griffiths ya tura sakonnin da suka haura 2,000 cikin makonni uku ga Mis Treharne da kuma wata mata ta daban.

Mis Treharne ta a ko da yaushe ita "ita tana tambayrsa game da abubuwan da yake so" amma zantawarsu kan "kan komawa kan jima'i ne a ko da yaushe".

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Andrew Griffiths bya nemi afuwa da wahalar da ya sanya matarsa a ciki

Mr Griffiths ya ce shi ya bi dokar da'ar jam'iyyar Conservative Party bayan ya tatatuna da jami'in ladabtarwa.

Wakilin BBC kan harkar siyasa Iain Watson ya ce Mr Griffiths, wanda ya yanke shawarar yin murabus a daren Juma'a "ya yi tsalle kafin a tura shi".

Mr Griffiths, mai shekara 47, wanda ya kasance dan majalisa tun shekarar 2010, kuma a cikin watan Afrilu ne matarsa ta fara haihuwa da 'ya.

Labarai masu alaka