Abubuwa goma da ya kamata ku sani game da Kayode Fayemi

Fayẹmi ati Buhari Hakkin mallakar hoto @kfayemi
Image caption Fayemi ya taka rawar gani a yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015

John Olukayọde Fayemi wanda ya yi takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar APC shi ne wanda hukumar INEC ta ayyana a matsayin sabon gwamnanjihar Ekiti.

  • An haifi John Olukayode Fayemi ranar tara ga watan Fabrairu na shekarar 1965 a garin Iṣan- Ekiti,da ke karamar hukumar Oye Ekiti ta jihar Ekiti.
  • Ya halarci makarantar Christs'School a garin Ado Ekiti tsakanin shekarar 1975 zuwa 1980.
  • Ya yi karatu a bangaren tarihi da harkokin diflomasiyya a jami'ar Legas da ta Ife (OAU).
  • Ya kuma yi karatun digirin digirgir kan yaki a King's Collegeda ke jami'ar Landan a Ingila.
  • John Kayode Fayemi ya yi bautar kasa a makarantar 'yan sanda da ke Sakkwato a arewacin Najeriya.
  • Ya yi aikin koyarwa a nahiyar Afirka da Turai da kuma Asiya
  • Haka kuma yi aiki a matsayin malami mai ziyara a kan harkar tsaro kan kasashen bakar fata a jami'ar tsaro taNational Defense University, a Amurka.
Hakkin mallakar hoto Kayọde Fayẹmi/Facebook
Image caption Fayemi ya yi ministan ma'adinai a gwamnatin shugaba Buhari daga shekarar 2016 zuwa 2018
  • Ya kasance mai bayar da shawara na musamman ga kwamitin bincike da sasantawa kan tauye hakkin bil Adama da aka yi wa lakabi da Oputa Panel wanda gwamnatin Olusegun Obasanjota kirkiro a shekarar 1999.
  • Ya yi aiki da ma'akatu kamar Africa Research and information Bureau ta Landan tsakanin shekara1991 zuwa 1993, da Deptford City Challenge, a Landan a shekarar 1993 zuwa 1995.
  • Ya taba zama gwamnan jihar Ekitia shekarar 2010 zuwa 2014, bayan hakan ne kuma ya yi ministan ma'adinai a gwamnatin shugaba Buhari daga shekarar 2016 zuwa 2018.

Labarai masu alaka