PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Ekiti

PDP logo Hakkin mallakar hoto PDP

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato PDP, ta yi watsi da sakamakon zaben jihar Ekiti da hukumar zabe ta sanar a ranar Lahadi.

PDP ta ce, jam'iyya mai mulki da INEC da jami'an tsaro ne suka hada baki wajen yi mata murdiya.

A saboda haka PDP ta ce fashi aka yi mata.

Mai magana da yawun shugaban jam'iyyar ta PDP Uche Secondas wato Shehu Yusuf Kura, ya shaida wa BBC cewa, ba su yarda da sakamakon wannan zabe ba.

Ya ce 'Wannan zabe an yi shi ne da son zuciya, saboda anyi amfani da jami'an tsaro da hukumar zabe sannan kuma wasu gwamnoni sun shiga cikinsa'.

Shehu Yusuf Kura ya ce, sam PDP ba ta lamunci sakamakon ba, don haka za ta dauki duk wani mataki da ya kamata ta dauka don kwatowa al'ummar jihar Ekiti 'yancinsu.

Mai magana da yawun shugaban jam'iyyar ta PDP, ya ce, zabe da kuma sakamakon zaben jihar Ekiti ya sa musu shakku a zukatansu a kan zaben 2019.

Karin bayani

John Olukayọde Fayemi, wanda ya yi takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar APC shi ne wanda hukumar INEC ta ayyana a matsayin sabon gwamnan jihar Ekiti.

Jam'iyyar ta APC ta samu yawan kuri'un da ya kai 197,459, yayin da jam'iyya mai mulki a jihar wato PDP ta samu kuri'u 178,121.

Jam'iyyu 35 ne suka fafata a zaben, to amma karawar ta fi zafi a tsakanin jam'iyyar PDP mai mulki da kuma jam'iyyar adawa ta APC a jihar.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/KAYODE FAYEMI

Karanta wasu karin labaran