Mutum miliyan 850 na fama da karancin ruwan sha a duniya

Ruwan sha Hakkin mallakar hoto Quora

Wata kungiyar ta kasa da kasa ta yi gargadin cewa duniya na fuskantar matsalar ruwan sha saboda gwamnatoci ba su kashe kudaden da suka kamata wajen samar da tsaftataccen ruwa ga al'umma.

Kungiyar mai suna Water Aid, ta ce matukar gwamnatoci ba su kara kudin da suke kashewa kan samar da ruwa da dala biliyan 28 ba, to kuwa ba za a cimma kudurin majalisar dinkin duniya na samar da tsaftataccen ruwan sha ga mutane nan da shekara ta 2030 ba.

Kungiyar ta ce yanzu haka mutane miliyan 850 ne ke fama da karancin tsaftataccen ruwa a doron kasa.

Wani rahoton Bankin Duniya ya ce yawan mutanen da ke rayuwa ba tare da tsabtataccen ruwan sha ba sun karu.

Sai dai a India da China ne rahoton ya ce yawan mutanen suka fi yawa, amma idan aka yi la'akari da yawan jama'a, matsalar ta fi tsanani a Afrika, musamman a kasashen Eritrea da Uganda da Habasha da Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo da kuma Somalia.

A Najeriya ma dai ana fuskantar matsalar rashin ruwa mai tsafta, kuma rashin ruwa da muhalli mai tsaftar na haddasa mutuwar yaran da ba su kai shekara biyar ba a kasar.

Masharhanta dai na ganin batun cimma burin samar da ruwan sha mai tsabta da kuma wadatarsa a kasashen duniya wani babban kalubale ne ga hukumomi.

Karanta wasu karin labarai

Labarai masu alaka