Matar da ta zamo kashin-bayan nasarar Croatia

Shugabar Crotia Grabar-Kitarovic. Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugabar kasar Crotia Kolinda Grabar-Kitarovic, ita ce wadda duniya ta yi amanna cewa ta zamo kashin bayan nasarar da Croatia ta samu na zuwa wasan karshe a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka kammala a Rasha.

Kafafen yada labaru sun ta Magana kan shugabar, wadda ta kasance a koda yaushe ta na karfafa wa 'yan wasan Croatia gwiwa tun daga lokacin da aka fara gasar cin kofin duniya da aka kammala a Rasha.

Shugabar ta bi jirgin saman 'yan kasuwa tare da sauran al'umma, tana sanye da rigar 'yan kwallon kafar kasar kamar sauran masu sha'awar kwallon kafa na kasarta, zuwa Rasha domin kallon wasa.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/KOLINDA GRABAR-KITAROVIC

Ba Grabar-Kitarovic ce kawai shugabar da ta nuna goyon baya ga 'yan kasarta a lokacin gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha kawai ba, sai dai, yayin da sauran shugabannin kasashe ke zama a wuraren da aka ware wa manyan mutane, ita shugabar ta Croatia ba a nan ta tsaya ba, wannan shi ne abin da ya sanya ake ta labari a kan ta.

Akwai wani daki da 'yan tamaula kan shiga su canza kaya bayan kammala wasa.

Wannan bai dakatar da ita ba, domin bayan kammala wasan da Croatia ta yi nasara a kan Denmark a ranar 1 ga watan Yuli a bugun fenareti, shugabar kasar ta shiga wannan daki ta gaishe da mai horas da 'yan wasan, inda ta ba shi hannu suka gaisa, ta rungume shi, sannan ta gaishe da daukacin 'yan wasan kasar.

Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY IMAGES

Bayan nan kuma, duk wanda ya kalli wasan da Croatia ta doke kasa mai masaukin baki Rasha a ranar 7 ga watan Yuli, ya ga yadda shugaba Grabar-Kitarovic ta rinka tsalle ta na tafa wa 'yan wasan na kasarta, sai dai wani abu da mutane da dama ba su sani ba shi ne abin da ta yi bayan kammala wasan.

Bayan kammala wasan shugabar ta bi 'yan wasan har inda suke, inda tare suka rinka rawa suna murnar nasarar da suka samu.

Tana aikawa da sako idan ba ta samu zuwa ba

Lokacin da shugabar ta halarci taron kwamitin tsaro na NATO a dai-dai ranar da Croatia ta kara da Ingila, ta rinka bibiyar yadda wasan ke kasancewa, sannan ta aika wa 'yan wasan da sakon fatan alheri.

Shugaba Kolinda Grabar-Kitarovic, ita ce shugabar kasa ta 4 a Croatia, kuma ita ce shugaba mafi karancin shekaru, kuma mace ta farko da ta mulki kasar.

Croatia dai ta kammala gasar ce a matsayi ta biyu, bayan da ta sha kashi a hannun Faransa da kwallo 4 da 2.

Labarai masu alaka