Obama ya ziyarci tsohon 'gidansu' a Kenya

Obama da Kenuyatta Hakkin mallakar hoto Reuters

Jama'a a kauyen Kogelo na yammacin Kenya sun kasance cikin murna saboda ziyarar da fitaccen dansu, tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya kai a karon farko cikin shekara 12.

Rabon Mista Obama da kauyen - inda kakanninsa su ke, tun shekarar 2006 lokacin da yana dan majalisar dattawa a Amurka.

Shirin, wanda ake kira Cibiyar Sauti Kuu, ya kunshi wani wurin motsa jiki ne da kuma cibiyar koyon sana'o'i.

Kusan za a iya cewa ba a kwarmata ziyarar ta Mista Obama ba a wannan karon idan aka kwatanta da wacce ya kai a 2015 lokacin yana kan karagar mulki.

Ya gana da Shugaba Uhuru Kenyatta a ranar Lahadi a birnin Nairobi.

Gidan talabijin na NTV ya wallafa wani bidiyon Mista Obama yana rawa lokacin da aka saki wani kida a wurin taron da yake halarta a kauyen na Kogelo.

Kafafen yada labaran kasar sun ce an tsaurara matakan tsaro a yankin amma hakan bai hana jama'a sayar da kayayyakin da ke da alaka da ziyarar ba, ciki har da masu dauke da tutar Amurka.

Wani abu da ke jan hankalin jama'a shi ne rahotan da wata jarida a Tanzaniya ta fitar wanda ya nuna cewa Mista Obama ya shafe kwana takwas tare da iyalansa a fitaccen wurin shakatawar nan na Serengeti National Park kafin ya isa Kenya.

Editan kasuwanci na BBC ya wallafa wasu kanun labarai na jaridu wanda wasu 'yan Kenya ke gani a matsayin wata murna da 'yan Tanzaniya ke yi:

Mista Obama zai wuce zuwa Afirka Ta Kudu domin gabatar da kasida a wurin bikin tunawa da mutuwar Nelson Mandela ranar Laraba.

Labarai masu alaka