Hotunan yadda Faransawa ke murnar lashe kofin duniya

Magoya bayan Faransa na murna a gaban benen Eiffel Tower a birnin Paris, 15 ga Juli 2018
Bayanan hoto,

Magoya bayana Faransa na murna a gaban Eiffel Tower

Magoya bayan Faransa sun rika murna bayan da tawagarsu ta doke Croatia da ci 4-2 a karawar kashe a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018.

Ta kasance ranar farin ciki ga duk 'yan wasan, sai dai Didier Deschamps ba zai taba mantawa da ranar ba, saboda ya zamo mutum na uku a tarihi da ya dauki kofin duniya yana dan wasa da kuma koci.

Bayanan hoto,

Magoya bayan Croatia na kallon wasan karshe na tawagarsu a gasar cin kofin duniya

An dakatar da wasan na takaitaccen lokaci bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci yayin da jami'ai suka fitar da wasu mutune hudu da suka shigo cikin filin.

Kungiyar masu fafutuka ta Pussy Riotdaga bisani ta wallafa sanarwar a shafinta na Facebook, inda ta dauki alhakin kawo cikas a wasan, wanda shugaba Vladimir Putin ya halarta.

Bayanan hoto,

Daya daga cikin masu zanga-zanga na kungiyar Pussy Riot, na tafawa da dan wasan Faransa Kylian Mbappé, kafin daga biani a taso keyarta waje

Bayanan hoto,

Dan wasan Faransa Paul Pogba na murna tare da abokan wasansa bayan ya zira kwallo ta uku daga cikin kwallaye hudu da Faransa ta ci

Bayanan hoto,

Kocin Faransa Didier Deschamps na murna tare da tawargarsa, bayan shekara 20 da ya jagoranci Faransa ta yi nasarar cin kofin duniya yana kyaftin

Bayanan hoto,

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na farin ciki kan nasarar da kasarsa ta samu yayin da takwararsa ta Croatia, Kolinda Grabar-Kitarovic, ta tsaya tana kallo

Hoton da ke kasa da ke nuna Shugaba Macron yana murna ya yadu kamar wutar daji, inda wasu masu amfani da shafukan sada zumunta ke shawartar shugaban ya yi amfani da hoton wajen yakin neman zabensa na gaba.

Bayanan hoto,

Dubban magoya bayan Faransa sun hau tituna suna shewa a birnin Paris bayan da 'yan wasan kasar suka yi nasara

Bayanan hoto,

Dan wasan Croatia Sime Vrsaljko na cikin dimuwa bayan da suka sha kaye

Bayanan hoto,

'Yan wasan Croatia na ba juna hakuri bayan da suka sha kaye

Sai dai daya daga cikin abubuwan da suka ja hankalin mutane shi ne lokacin da aka fara ruwan sama inda aka bai wa Shugaba Putin lema, inda aka bar shugabannin Faransa da Croatia suka jike lokacin da aka zo mika kofin.

Bayanan hoto,

Shugaba Macron na Faransa da shugaba Grabar-Kitarovic ta Croatia sun kasance cikin raha kuma kusa da juna har aka kamala bikin mika kofi

Mutane sun bayyana ra'ayoyinsu a kafofin sada zumunta daban-daban kan yadda shugaba Putin ya ki amfani da lemarsa tare da takwarorin aikinsa na Faransa da Croatia.

Bayanan hoto,

Ruwan sama da rashin lema ba su hana shugabannin Faransa da Croatia gaisawa da 'yan wasansu ba

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.