Zaben Ekiti: An shamu mun warke - PDP

PDP logo

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta gargadi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyarsa ta APC kar su yi zaton cewa 'yan kasar sun amince da "magudin da suka yi" a zaben jihar Ekiti.

A wata sanarwa da jam'iyyar PDP ta fitar ranar Litinin, ta ce Shugaba Buharin ya yi abun kunya wajen bari a "tafka magudi" a zaben, duk da cewa yana kiran kansa mai yaki da cin hanci da rashawa.

Zuwa yanzu dai gwamnatin Buhari ba ta mayar da martani kan wannan zargi na PDP ba.

A ranar Lahadi ne hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben jihar Ekiti da aka yi ranar Asabar, wanda Kayode Fayemi na jam'iyyar APC ya lashe.

PDP ta kuma ce: "A yayin da muke kokarin kwato hakkinmu da ake kwace, muna jaddada cewa wannan ne karo na karshe da PDP za ta amince a take mata hakkinta a kowane mataki na kowane zabe."

Ko a wata hira ma da mai magana da yawun shugaban jam'iyyar ta PDP Uche Secondas wato Shehu Yusuf Kura, ya shaida wa BBC cewa a ranar Litinin da safe, ya ce ba su yarda da sakamakon wannan zabe ba.

PDP ta ce, jam'iyya mai mulki da INEC da jami'an tsaro ne suka hada baki wajen yi mata murdiya.

A saboda haka PDP ta ce fashi aka yi mata.

Ya ce 'Wannan zabe an yi shi ne da son zuciya, saboda anyi amfani da jami'an tsaro da hukumar zabe sannan kuma wasu gwamnoni sun shiga cikinsa'.

Shehu Yusuf Kura ya ce, sam PDP ba ta lamunci sakamakon ba, don haka za ta dauki duk wani mataki da ya kamata ta dauka don kwatowa al'ummar jihar Ekiti 'yancinsu.

Mai magana da yawun shugaban jam'iyyar ta PDP, ya ce, zabe da kuma sakamakon zaben jihar Ekiti ya sa musu shakku a zukatansu a kan zaben 2019.

Karin bayani

John Olukayọde Fayemi, wanda ya yi takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar APC shi ne wanda hukumar INEC ta ayyana a matsayin sabon gwamnan jihar Ekiti.

Jam'iyyar ta APC ta samu yawan kuri'un da ya kai 197,459, yayin da jam'iyya mai mulki a jihar wato PDP ta samu kuri'u 178,121.

Jam'iyyu 35 ne suka fafata a zaben, to amma karawar ta fi zafi a tsakanin jam'iyyar PDP mai mulki da kuma jam'iyyar adawa ta APC a jihar.

Karanta wasu karin labaran