An kashe kadoji 300 don daukar fansa

Kadodjin da aka kashe don daukar fansa Hakkin mallakar hoto Reuters

Wasu mazauna wani kauye sun kashe kadoji 300 a wani wuri da aka kebe don kare dabbobi da ke lardin West Papua a kasar Indonesia.

Mutanen sun kashe kadojin ne ta hanyar yanka su a wani mataki na ramuwar gayya bayan da daya daga cikin dabbobin da ke wannan wuri ta kashe daya daga cikin mazauna yankin.

Mahukunta da 'yan sanda sun ce sun gaza hana mutanen aikata abinda suka yi saboda yadda suke a fusace.

Kisan wata dabba da aka kebe a Indonesia babban laifi ne, wanda ke sa aci tarar mutum ko kuma ya zauna a gidan yari.

Kadar ta kashe mutumin ne a lokacin da ya ke cirar ganyayyaki a wata gona da ake kiwon kadoji.

Wani dake kula da wajen ya ce ya jiyo ihun mutum na neman taimako, ko da yaje wajen sai ya kada ta kai masa cafka.

Bayan an binne mutumin ne, sai 'yan garin da kadar ya kashe suka taru a fusace suka je wajen da ake kiwon dabbobin dauke da wuka da shebir da kuma guduma.

Da isarsu sai suka afka cikin wajen suka rinka janyo kadoji suna yanka su.

Karanta wasu karin labarin

Labarai masu alaka