Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 40 a Katsina

Governor Masari
Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari lokacin da ya kai wa al'ummomin da abin ya shafa ziyara

Akalla mutum 40 ne suka mutu sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka shafe sa'o'i ana yi a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Ruwan kamar da bakin kwarya ya sa dam din garin Jibya da madatsar ruwar garin suka cika suka tumbatsa, sannan suka yi ambaliya.

Hukumomin agaji a jihar sun shaida wa BBC cewa fiye da mutane 2,000 ne zuwa yanzu aka tantance sun rasa matsugunnansu.

An yi asarar dimbin dukiya yayin da ruwan ya yi awangaba da gawarwakin mutane zuwa Jamhuriyar Nijar, mai makwaftaka da yankin.

Jami'ai sun ce a yanzu an fara debo gawarwakin, kuma ana tsugunar da wadanda lamarin ya shafa a makarantu.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar, Alhaji Aminu Waziri, ya shaida wa BBC cewa, gidaje fiye da 200 sun rushe kuma tuni aka kai mutane da suka rasa matsugunnan nasu makarantar firamaren da ke garin na Jibiya domin su zauna kafin a samar musu matsugunni.

Ya ce ambaliyar da dam din Jibya ya yi ita ce ta sa ruwa ya shiga gidajen jama'a, musamman wadanda ke kusa da madatsar ruwan.

Daga nan ne aka samu wannan asara ta dukiya da kuma rayuka, in ji shi.

Ko a watan daya gabata, an samu ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomi na jihar da suka hada da Katsina da Charanchi da kuma Musawa, lamarin da ya janyo asarar rayuka da kuma dukiya.

Ana dai samun irin wannan matsala ta rushewar gidaje da kuma asarar rayuka a wasu sassa na Najeriya sakamakon ruwan saman da awani lokaci ya ke zuba kamar da bakin kwarya.

Karanta wasu karin labaran