An hana 'yar majalisa shiga dakin otal da mijinta

An hana Catherine daki ne saboda ba ta gabatar da shidar aure ba

A kasar Kenya an hana wata 'yar majalisa daki a wani otal saboda ba ta nuna shaidar ita matar aure ce ba.

Masu kula da otel din da ke garin Kericho a yankin Rift valley sun soke dakin da Catherine Waruguru ta kama tare da mijinta, bayan ta gaza nuna musu hujjar cewa mutumin da suke tare, mijinta ne.

Lamarin dai ya harzuka 'yar majalisar mai wakiltar yankin Laikipia.

A karkashin dokokin otel din dai ba a yarda mace da namiji su karbi daki guda ba, sai dai idan ma'aurata ne.

Bayan wannan al'amari dai 'yar majalisar ta kira wani taron manema labari, ta kuma shaida wa BBC cewa ta fadi wa jami'an otal din cewa namijin da ke tare da ita mijin aurenta ne, amma duk da haka suka ki amincewa.

Ta kuma yi zargin cewa yana iya yiwuwa akwai makarkashiya ta siyasa dangane da wannan abu da ya faru da ita a otal din.

Ta ce "Wannan abu ne maras kyau, wanda ya yi kama da siyasa ko kabilanci, kuma ci baya ne. Muna ganin su mutane ne da ke nuna banbanci a kan mata".

Ta kuma soki irin wannan doka ta otal din, domin a cewar ta jami'an ba su da wata hanya ta tantance sahihancin kasancewar mutane ma'aurata ne ko kuma a'a.