Mun yi hannun-riga da APC – Gwamnan Benue Samuel Ortom

Governor Samuel Ortom
Bayanan hoto,

Samuel Ortom yana takun-saka da Sanata George Akume

Gwamnan jihar Benue ya ce jam'iyyar APC wacce a karkashinta ya hau kan mulki, ta ba shi jan kati, a don haka ba ya cikinta.

Samuel Ortom ya shaida wa jami'an gwamnatinsa da jama'ar jihar cewa a kasuwa ya ke domin ba shi da wata jam'iyya a yanzu.

Da yake magana a ranar Litinin lokacin rantsar da wani sabon mai ba shi shawara, ya ce "a game da batun jam'iyya, ni an ba ni jan kati a don haka ina wajen fili... ".

Mr Ortom ya kara da cewa "jan katin da APC ta bashi zai bashi damar komawa duk jam'iyyar da ya ga ta dace da akidun gwamnatinsa".

Masu lura da al'amura na alakanta wannan mataki da tabarbarewar dangantaka tsakanin gwamnan da Sanata George Akume, wanda ake ma kallon shi ne ke da iko da jam'iyyar a jihar.

Sabanin da ke tsakanin mutanen biyu ya kara kamari ne bayan zabukan shugabannin jam'iyyar da aka gudanar a kwanakin baya.

Yunkurin sasantawa

Sai dai shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole, ya yi watsi da rahotannin da suke cewa Gwamna Ortom ya bar jam'iyyar, yana mai cewa ba su da tushe.

A daren ranar Litinin ne kuma aka bayyana cewa uwar jam'iyyar ta gayyaci gwamnan da kuma Sanata Akume zuwa Abuja domin tattaunawa kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar a jihar.

Jami'yyar dai na fama da rikice-rikice a sassan kasar da dama, lamarin da ya kai ga bullar wani bangaren rAPC da ya yi ikirarin yin tawaye tare da kafa nashi tsarin shugabancin.

Bangaren, wanda ke karkashin jagorancin Buba Galadima, na samun goyon bayan wasu gaggan jam'iyyar da ke rike da mukamai a matakai daban-daban.

Wannan sabuwar rigimar da ta sake tasowa jam'iyyar a Benue na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar zabe ta bayyana APC a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna mai muhimmanci da aka gudanar a jihar Ekiti.

Masu sharhi na ganin idan har jam'iyyar ba ta yi sauri wurin dinke wannan baraka ba, to hakan zai iya bai wa sauran 'ya'yanta da ke kan katanga kwarin gwiwar ficewa daga jam'iyyar a daidai lokacin da ya rage watanni a gudanar da zabukan kasa baki daya.

Wadanda suka fice daga APC a kwanan nan

Bayanan sauti

Jam'iyyar APC ta kauce hanya - Buba Galadima

  • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
  • Suna dai samun goyon bayan Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi
  • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
  • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa - kamar yadda Daily Trust ta rawaito
  • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
  • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.