Jami'an tsaro za su sa wa masu yawan mabiya a Facbook ido

Abdulfatah Hakkin mallakar hoto Getty Images

Majalisar dokoki ta Masar ta amince da wata sabuwar doka da za ta sa ido kan kafafan sada zumunta na zamani, lamarin da ya janyo fargabar cewar dokar za ta hana sukar Shugaba Abdul-Fatah al-Sisi.

Dokar ta ce duk wanda ke amfani da kafofin sada zumunta kuma yana da mabiya sama da 5,000 zai kasance daya daga cikin wadanda Majalisar Koli ta Masar kan watsa labarai ke saka wa ido.

kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato dokar na cewa za ta bai wa majalisar ikon dakatar ko toshe duk wani shafi na mutum wanda "ke wallafa ko watsa labaran karya ko wani abu da ke tunzura mutane ga tashin hankali da kuma kiyayya."

Wannan doka za ta shafi shafukan itanet da shafukan 'bulog' da kuma shafukan sada zumunta.

Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewar, wasu kungiyoyi masu kare hakkin bil Adama suna ganin dokar da har yanzu na jiran amincewar Mista Sisi a matsayin wani yunkuri na takaita amfani da shafukan sada zumunta wanda shi ne kadan daga cikin kafofin tofa albarkacin baki da ya rage a kasar Masar.

Dokar- tare da wasu dokokin da ke da alaka da kafofin watsa labarai- zai halasta "hana mutane fadan albarkacin baki tare da matsa kaimi wajen yakar 'yancin fadan albarkacin baki a kasar Masar," in ji jaridar Najia Bounaim ta Amnesty International da ke Amurka.

Labarai masu alaka