Wane tasiri zaben Ekiti zai yi ga 2019?

PDP Hakkin mallakar hoto @PDPOFFICIALNIG
Image caption 'Yan jam'iyyar PDP sun gudanar da zanga-zanga a gabannin zaben jihar Ekiti a Abuja

Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Ekiti ta sha kaye a zaben gwamnan da aka yi a jihar ranar Asabar.

Dan takarar gwamna a jam'iyyar APC, Kayode Fayemi, ya doke dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP Kolapo Olusola-Eleka.

Kayen da PDP ta sha a zaben ya bai wa mutane mamaki ganin yadda ta doke APC a zaben gwamnan jihar a shekarar 2014.

A zaben shekarar 2014 dai Ayodele Fayose na PDP ne ya yi nasara bayan ya doke Kayode Fayemi na APC.

Koma-bayan siyasa

Akwai wadanda suke ganin kayen da babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta sha a Ekiti ya jawo mata koma-baya ta fuskoki daban-daban.

Jam'iyyar ta rasa mulki ke nan a duka jihohi shidan da ke yankin kudu maso yammacin kasar.

Bayan PDP ta kayar da APC a zaben 2014, ita jam'iyyar PDP tana da jihohi biyu ne a yankin, wato Ekiti da Ondo.

Sai dai kuma PDP ta rasa jihar Ondo a zaben gwamnan da aka gudanar a watan Nuwanban shekarar 2016 wanda Rotimi Akeredolu ya lashe.

A yanzu haka dai jam'iyyar ba ta da wata jihar da take iko da ita a yankin.

'Masu komawa PDP za su karaya'

Har ila yau akwai wadanda suke ganin shan kayen PDP a Ekiti zai karya wa wadanda suke son komawa jam'iyyar gwiwa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kafin zaben Ekiti, masana da dama suna hasashen wasu 'yan jam'iyyar APC mai mulkin kasar da ke neman ficewa daga jam'iyyar suna son komawa jam'iyyar PDP ne.

Cikin masu son kamowa jam'iyyar PDP din dai akwai wadanda tsaffin 'yan jam'iyyar PDP da suka koma APC gabanin zaben shekarar 2015.

Suna ganin ita jam'iyyar za ta fara samun karbuwa daga wajen 'yan kasar ganin irin halin da suka ce ake ciki a kasar karkashin gwamnatin jam'iyyar APC.

Sai dai kuma wannan kayen zai iya karya wa irin wadannan mutanen gwiwar koma wa jam'iyyar PDP.

Amma kuma akwai wadanda suke ganin zaben ba zakaran gwajin dafin babban zaben shekarar 2019 ba ne.

Wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Malam Bashir Baba, yana cikin masu irin wannan tunanin.

Ya ce: "Yanzu halin da ake ciki, 'yan Najeriya sun farga. Sun fahimci yadda siyasar take ta yadda ba jam'iyya suke kallo ba yanzu. Dan takara suke kallo."

Karfin PDP a siyasar kasa

Idan aka zo zaben kasa, jam'iyyun siyasa masu gwamnati a jihohi na da damar iya samun tagomashi ta irin yadda suke yi wa mutanen jihar aiki.

Sai dai kuma Malam Bashir ya ce "babu wata jam'iyya guda daya da za ka daga mun ka ce mun an kafa ta ne bisa akida. Shigifu ne kawai ga su nan ga 'yan siyasa wadanda suke hankoran yin takarar mukamai."

Wannan na nufin idan har jam'iyya mai mulki a jihar ba ta gabatar da dan takaran da mutanen jihar suka amince da shi ba a zaben shugaban kasa, da wuya mulkin da jam'iyyar ke yi a jihar ya yi mata amfani a zaben kasa.

Mai fashin bakin ya kara da cewa irin dan takarar da jam'iyyar PDP ta gabatar a zaben shugaban kasa na shekarar 2015 ne ya sa ta sha kaye.

Kafin zaben gwamnan Ekiti da aka yi ranar Asabar da ta gabata dai jam'iyyar PDP ta yi ta nanata aniyyarta ta karbe mulki daga hannun APC mai mulkin kasar.

Shin rashin nasarar da ta yi a zaben zai iya saka shakku kan yiwuwar cimma burin na PDP na kwace mulki daga hannun APC a zaben shekarar 2019?

Za a iya samun amsar wannan tambayar daga yanzu zuwa lokacin zaben 2019.

Hakkin mallakar hoto @Fayose
Image caption Ayo Fayose na jam'iyyar APC shi ne gwamnan jihar Ekiti mai barin gado

Yaya PDP ta dauki sakamakon zaben?

Shin jam'iyyar za ta dauka cewa wannan na nufin mutanen jihar Ekiti ba su yarda da irin salon mulkinta ba ne, ko kuma yakin neman zabenta ne yake da matsala?

Amsar wadannan tambayoyin da ma wasu irinsu da kuma yadda jam'iyyar za ta sauya salon siyasarta gabanin zaben 2019 ka iya tasiri game da makomarta.

A halin yanzu dai gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce jam'iyyarsa ta PDP za ta je kotu domin neman ta bi mata hakkinta a zaben wanda ya ce an kayar da ita bisa magudi.

Sai dai kuma shari'ar zabe aba ce wadda ke daukar dogon lokaci, lokacin shari'ar kan dara shekara daya a lokuta da dama.

Jam'iyyar PDP tana matsa kaimi wajen sukar yadda gwamnatin APC ke gudanar da mulkinta kuma tana nuna cewa ita ce ta fi iya mulkin kasar.

Sai dai APC ta kan kalubalance PDP kan yadda ta kwashe shekara 16 suna mulkar kasar.

Jihohin da ke hannun PDP

 • Abia PDP
 • Akwa Ibom PDP
 • Bayelsa PDP
 • Cross River PDP
 • Delta PDP
 • Ebonyi PDP
 • Enugu PDP
 • Gombe PDP
 • Rivers PDP
 • Taraba PDP

Jihohin da ke hannun APC

 • Adamawa APC
 • Bauchi APC
 • Benue APC
 • Borno APC
 • Edo APC
 • Ekiti APC
 • Imo APC
 • Jigawa APC
 • Kaduna APC
 • Kano APC
 • Katsina APC
 • Kebbi APC
 • Kogi APC
 • Kwara APC
 • Lagos APC
 • Nasarawa APC
 • Niger APC
 • Ogun APC
 • Ondo APC
 • Osun APC
 • Oyo APC
 • Plateau APC
 • Sokoto APC
 • Yobe APC
 • Zamfara APC