Sambo Dasuki 'ya cika' sharuddan beli

Dasuki Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ana sa ran nan ba da jimawa ba hukumar tsaro ta farin kaya za ta saki tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro Kanal Sambo Dasuki mai ritaya, bayan da ya "cika" dukkan sharadin belinsa da kotu ta bayar.

Lauyan Kanal Dasuki, Ahmed Raji ya tabbatar wa BBC cewa, wanda yake karewar ya cika dukkan sharuddan da babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta sanya masa.

Mista Raji ya ce tun a ranar 2 ga watan Yuli ne babbar kotun tarayyar a Abuja ta bayar da umarnin sakin Kanal Dasuki, inda su kuma suka cika sharuddan belin ranar Juma'ar da ta gabata.

"Da ma sharuddan da kotun ta gindaya don bayar da beli sun hada da gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa sannan ya ajiye naira miliyan 100, kuma duk mun gabatar da wadannan abubuwa a ranar Juma'ar da ta wuce," in ji Mista Raji.

A yanzu dai lauyan ya ce kotun ta rubuta wasika zuwa ga hukumar DSS, tana mai ba ta umarnin sakin Kanal Dasuki.

Sai dai Mista Raji ya ce ba shi da tabbacin ainihin ranar da hukumar DSS za ta sallami Mista Dasukin, "amma na yi amanna cewa hukumar za ta bi umarnin kotun."

"Hukuma ce mai bin tsarin doka da oda wacce kuma nake matukar girmamawa, ina sa ran ba za ta ki bin umarnin kotu ba, amma dai ban san takaimaimiyar ranar da za su sake shi ba,' a cewar Mista Raji.

Hukumar DSS dai tana rike da Mista Dasuki tun a watan Disambar 2015.

Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ce ta bayar da belin Dasuki a ranar 2 ga watan Yulin, a wata karar da ya kai kan kare hakkinsa na dan Adam.

Mista Dasuki ya nemi kotun ta tilasta wa gwamnatin tarayya ta bi dukkan umarnin kotun da aka bayar na sakinsa.

Sau hudu dai kotun tarayyar na bayar da belinsa a baya, haka kuma kotun ECOWAS ma ta bayar da belin nasa sau daya.

Gwamnatin dai ta dade tana cewa tana ci gaba da rike shi ne saboda ta daukaka kara.

A yanzu dai babu tabbas kan ko hukumar DSS za ta amince da sakin nasa ganin cewa ya cika sharuddan belin ko koma a'a.

Labarai masu alaka