Ya kamata Dangote da BUA su rage farashin siminti – Osinbajo

osinbajo

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci manyan 'yan kasuwar nan biyu da ke da kamfanonin siminti, Alhaji Aliko Dangote da mai kamfanin BUA da su rage farashinsa a kasar.

Mista Osinbajo ya yi wannan kira ne a yayin da yake kaddamar da Kamfanin Siminti na BUA da ke Kamalbaina a jihar Sokoto.

Ya ce siminti babban ginshiki ne na bunkasa tattalin arziki yana kuma da muhimmanci wajen bunkasa ababen more rayuwa da ke ciyar da tattalin arziki gaba.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa ana bukatar siminti wajen gina tituna da kuma amfani da shi wajen magance matsalar rashin isassun gidaje miliyan 17 da aka kiyasta.

A yayin da yake kaddamar da kamfanin, Farfesa Osinbajo ya bayyana shi a matsayin wata karuwa da gwamnatin tarayya ta samu a kokarinta na samar da wadataccen siminti.

Shugaban kamfanin BUA Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u ya ce kamfanin yana da wasu abubuwa da wasu kamfanoni kishiyoyinsa ba su da shi.

Kamfanonin Dangote da na BUA na daga cikin manyan kamfanonin da ke samar da siminti a Najeriya.