Matar da likita ya kara wa girman duwawu ta mutu

Dr Denis Likitan da ke aikin karawa mata wasu sassa na jikinsu.

A kasar Brazil yanzu haka jami'an tsaro na can na neman wani likitan fida da aka fi sani da Dr Bumbum, wanda ya kware wajen yi wa mutane aiki ko alluran da za su kara wani bangare a sassan jikinsu.

Ana neman likitan ne bayan ya arce sakamakon mutuwar wata mata bayan ya yi mata allurar da zata kara mata girman mazaunai wadda daga baya kuma aka samu akasi.

Yanzu haka dai 'yan sanda na bincike a kan lamarin wanda ake zargin cewa likitan ya aikata abubuwa da dama da basu dace ba.

Likitan mai suna Dr Denis Furtado, mai kimanin shekara 45 da haihuwa,na da masu bibiyarsa a shafukansa na sada zumunta da suka hadar da Facebook da Twitter da suka kai kusan dubu 700, saboda yadda ya ke saka hotunan mutanen da ya yi wa aiki, kafin ayi aikin da kuma bayan an yi aikin ko allurar.

Dr Bumbum dai ya kware ne wajen yin aikin da zai kara wasu sassa na jikin dan adam musamman mata.

'Yan sanda na neman sa ruwa a jallo saboda mutuwar wata mata Lilian Calixto mai kimanin shekara 46 da ta yi tattaki ta je har kasar ta Brazil domin ayi mata aiki don mazaunanta su kara girma.

Lilian dai ma'aikaciyar banki ce, kuma ta na da aure da kuma 'ya'ya biyu.

Ta kuma je ayi mata aikin kara mazaunan ne domin kwalliya da kara kyau.

Likitan dai na zaune ne a wani gida tare da mahaifiyarsa da kuma budurwarsa wadda ma'aikaciyar jinya ce.

Kuma yawanci a gidansa ya ke yi wa matan aiki, domin itama wannan mata da ta mutu bayan ya yi mata allurar, a gidansa ya yi mata.

Matar ta mutu ne bayan an samu matsala a allurar kara mata girman mazaunai a ranar Lahadin da ta gabata.

Tuni dai aka kama budurwar ta sa ma'ikaciyar jinya wadda ake zargi sun yi aikin tare.

Karanta wasu karin labaran