Kotu ta ci tarar BBC kan keta sirrin wani mawaki

Sir Cliff Hakkin mallakar hoto Victoria Jones/PA Wire
Image caption Sir Cliff Richard ya ce ya ji dadin hukuncin kotun

Fitaccen mawakin nan na Birtaniya Sir Cliff Richard ya yi nasara a shari'ar da ya shigar kan yadda BBC ta bayar da labarin samamen da 'yan sanda suka kai gidansa.

Alkalin din babbar kotu Mai shari'a Mann ya umarci a biyashi diyyar fam 210,000.

BBC ta ce ma'aikatanta sun yi aiki ne da zuciya daya kuma tana duba yiwuwar daukaka kara.

Mawakin ya bayyana cewa rahoton da BBC ta yi a kan samamen a shekarar 2014, wanda wani bangare ne na binciken da aka yi kan zargin lalata da kananan yara, "ya yi matukar keta sirrinsa".

Ba a dai kama ko tuhumci Sir Cliff ba kan wannan zargi wanda ya samo asali tun shekarar 1985.

Mai shari'ar ya ce BBC ta wuce gona-da-iri wurin keta sirrin Sir Cliff a yunkurinta na sa labari ya yi armashi.

Ya yi watsi da hujjar BBC ta cewa ta wallafa rahoton ne a karkashin dokar 'yan cin fadin albarkacin baki da kuma na 'yan jarida.

'Matukar murna'

Alkalin ya sa a bawa Sir Cliff diyyar fan 190,000 da kuma karin 20,000 bayan da BBC ta gabatar da labarin domin neman lambar yabo.

Ya kara da cewa dole ne BBC ta biya kashi 65 cikin 100 na kudin sannan 'yan sandan yankin South Yorkshire da suka kai samamen su biya kashi 35 cikin 100.

Jim kadan bayan bayyana hukuncin kotun, Sir Cliff ya ce ya yi farin ciki, sannan ya kara da cewa: "Labari ne mai dadin ji."

Labarai masu alaka