Jirgin saman Habasha ya yi tafiyar tarihi zuwa Eritrea

Passengers are welcomed by cabin crew inside an Ethiopian Airlines flight who departed from the Bole International Airport in Addis Ababa, Ethiopia, to Eritrea"s capital Asmara on July 18, 2018 Hakkin mallakar hoto AFP

An raba furranni da barasa a tafiyar jirgin farko, cikin shekara 20, da ya dauki fasinja daga Habasha zuwa Eritrea.

kamfanin jiragen kasar Habasha ya ce "tsuntsunta ta zaman lafiya" ta tashi zuwa Eriteria bayan an kawo karshen yanayin yaki tsakanin kasashen.

Matukin jirgi Yosef Hailu ya fada wa BBC cewa yana cikin matukar farin ciki.

Ana sa ran za a sada 'yan uwa da abokai a karon farko cikin tun da aka yi yakin kan iyaka na shekarar 1998 zuwa 2000 ya hana sifiri ta sama da ta kasa tsakanin kasashen biyu.

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya jagoranci tattaunawar zaman lafiya da Eritrea tun ya dare mulki a watan Afrilu.

Ya Kuma ya rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya da kawance da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki a ranar 9 ga watan Yuli wadda ta ayyana karshen "yanayin yaki".

An sanya hannu a kan yarjejeniyar a babban birnin kasar Eriteria, Asmara, yayin ziyarar farko na shugaban Habasha cikin shekara 20.

Mista Isaias ya ziyarci Etopia bayan kimanin mako guda.

Shugabannin biyu sun amince su dawo da huldar diplomasiyya da kuma harkar sufuri ta sama da ta kasa tsakanin kasashen biyu.

Labarai masu alaka