Tsohon babban alkalin Najeriya Aloysious Katsina-Alu ya rasu

Katsina-Alu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marigayi Aloysious Katsina-Alu dan asalin garin Ushongo ne da ke jihar Benue ta tsakiyar kasar.

Tsohon babban alkalin Najeriya, Aloysious Katsina-Alu, ya rasu yana mai shekara 76.

Katsina-Alu ya kasance babban mai shari'a na kasar daga shekarar 2009 zuwa 2011, inda mai shari'a Dahiru Musdapher ya maye gurbinsa.

An samu rudani a lokacin da aka zo rantsar da shi saboda rashin lafiyar Marigayi Shugaba Umaru Yar'Adua da kuma rashin mika ragamar iko da shugaban bai yi ba ga mataimakinsa Goodluck Jonathan.

Wannan ne ya sa sabanin yadda aka saba, sai mutumin da ya gada ne, Mai Shari'a Idris Legbo Kutigi, ya rantsar da shi.

Marigayin dai dan garin Ushongo ne da ke jihar Benue ta tsakiyar kasar.

Mai Shari'a Katsina-Alu yana daga cikin alkalan da suka yi fice a fagen shari'ar Najeriya.

Ya dade ana damawa da shi, kuma wasu na yi masa kallon ya taka rawa wurin ci gaban fannin.

Sai dai a gefe guda wasu masu lura da al'amura sun soke shi da kasancewa cikin gungun alkalan da suka hana ruwa-gudu wurin kawo sauyi a fannin, wanda ya dade yana fuskantar suka.

Fannin shari'a a Najeriya ya yi kaurin suna wurin zargin cin hanci da rashawa da kuma kawo tsaiko wurin yakarsa da ma tabbatar da adalci a harkokin rayuwa a kasar.

Sai dai masu ruwa da tsaki a fannin sun sha musanta wadannan zarge-zarge.

Tarihin marigayin a takaice

  • A haife shi a ranar 28 ga watan Agustan shekarar 1941
  • Dan asalin garin Ushongo ne na jihar Benue
  • Ya zama babban mai shari'ar Najeriya a 2009
  • Ya gaji Mai Shari'a Idris Legbo Kutigi
  • Ya zama alkali a babbar kotun Najeriya a shekarar 1998

Labarai masu alaka