An sake kaddamar da kamfanin jirgin saman Najeriya a Birtaniya

Nigeria Air Hakkin mallakar hoto Twitter/Bashir Ahmad
Image caption An sake kaddamar da kamfanin jirgin ne a Birtaniya ranar Laraba

Ministan Harkokin Sufurin Najeriya Sanata Hadi Sirika ya kaddamar da sabon kamfanin jirgin saman Najeriya a wani bikin baje kolin jiragen saman a kasar Birtaniya.

Ya ce zuwa watan Disamban bana ake fatan kamfanin jiragen saman na Najeriya zai fara aiki.

Har ila yau ya ce kamfanin zai rika zirga-zirga kashi uku a tsakanin kasashe 81, wanda ta kunshi ta cikin gida da yankin Afirka ta Yamma da kuma sauran kasashen duniya.

"Najeriya za ta iya. Kuma muna so mu yada al'adunmu da tarihinmu. Hakan zai bayar da damar bunkasa tattalin arziki da ayyukanyi," in ji shi.

Sai dai batun farfado da kamfani jiragen saman na Najeriya na hadin gwiwa ne da 'yan kasuwa, inda ministan ya ce ita ce hanyar kawai da ta fi dacewa da za a dauki lokaci ana cin moriyarsa.

Jama'ar Najeriya, kasar da ta fi karfin tattalin arziki a Afirka, na dogaro ne da kamfanonin jiragen 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Wasu na ganin farfado da kamfanin jiragen saman zai taimaka wajen samun saukin tsadar farashin tikitin shiga jiragen sama na 'yan kasuwa a kasar.

Ko da yake kamfanonin jiragen saman na cewa dole kujerar jirginsu ta yi tsada saboda yawan kudaden harajin da suke biyan gwamnati.

Za a iya samu wadatuwar jiragen saman zuwa wasu sassa na kasar da jiragen 'yan kasuwa ba su zuwa idan sabon kamfanin ya fara aiki.

A can baya Najeriya tana da kamfanin Nigeria Airways da ke zirga-zirga a kasar har zuwa kasashen waje, amma kamfanin ya durkushe saboda wasu dalilai da ke da nasaba da sakaci daga bangaren gwamnati wajen kula da lafiyar jiragen da kuma sakaci da aiki daga ma'aikata.

Durkushewar kamfanin ya haifar da rasa ayyukanyi ga ma'aikata da dama.

Labarai masu alaka