An 'kona' dakunan karatun da Dino Melaye ya gina a mazabarsa

Dino Melaye

Asalin hoton, Instagram/Dino

Bayanan hoto,

Sanata Dino Melaye ya nemi 'yan sanda da su zakulo wadanda suka aikata barnar

Sanatan da ke wakiltar Kogi ta Yamma ya yi Allah-wadai da kona wasu dakunan karatu da wasu 'yan banga suka yi wadanda ya ce ya gina a wata makaranta da ke mazabarsa.

Dino Melaye, wanda ya ziyarci makarantar Sakandaren ta Sarkin Noma, da ke birnin Lokoja ranar Laraba, ya yi alkawarin sake gina dakunan karatun nan take.

Har ila yau dan majalisar dattawan ya ce babu wata barazana da za ta hana shi gudanar da ayyukan ci gaba ga jama'arsa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Gwamnatin jihar da ma rundunar 'yan sanda sun yi tir da lamarin, wanda kawo yanzu ba a san wadanda suka yi ba, kuma babu wanda 'yan sanda suka kama tukuna.

Mai magana da yawun Gwamna Yahaya Bello, Kingsley Fanwo, ya ce gwamnati ta umarci jami'an tsaro da su nemo wadanda ke da alhakin wannan aika-aikar.

Mr Fanwo na magana ne bayan tawagar gwamnatin jihar ta kai ziyara makarantun da aka kai harin.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da mummunan takun saka tsakanin sanatan da kuma Gwamnan jihar Yahaya Bello.

Ko a kwananin baya an yi yunkurin yi wa sanatan, wanda ya yi kaurin suna uwrin janyo kace-nace, kiranye amma a karshe ya yi nasara duk da cewa yana kwance a gadon asibiti yana jinya a lokacin.

Sanatan ya wallafa hotunan abin da ya faru a shafinsa na Instagram inda ya ce "an kona dakunan karatun ne da misalin karfe 2.00 na dare".

Sanata Dino Melaye, wanda ya yi magana ga manema labarai bayan ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru, ya bayyana kona dakunan karatun da cewa "dabbanci ne da kuma rashin waye wa".

Ya kuma yi Allah-wadai da lalata wasu dakunan karatun hudu da ya gina a karamar makarantar Sakandare ta Lokongoma a Lokoja, sannan ya nemi 'yan sanda da su zakulo wadanda suka aikata wannan barnar.

Sanatan ya ce abin mamaki ne yadda mutane za su lalata kayan gwamnati saboda son zuciya, yana mai cewa abin kunya ne ga jihar wacce ta yi suna a fagen ilimi a arewacin Najeriya.

Ya kara da cewa abin da ya faru ba zai hana shi ci gaba da zagayen mako guda da ya fara ba, domin nuna godiya ga jama'ar da yake wakilta da kuma kaddamar da ayyuka 143 da ya ce ya yi a yankin, da suka kai na "naira biliyan bakwai."

Daga bisani sanatan ya kaddamar da wasu dakunan karatu da ya gina a makarantun firamare na Tawari da Manyare, da titi mai tsawon kilomita 10 da ya hada Manyare da Gegu Beki da mai tsawon kilomita 15 a hanyar Orehi da Irovomi, duka a karamar Hukumar Kogi.

Sanatan ya kuma yi kira ga jama'ar da aka yi wa ayyukan da su kare su daga miyagu domin jama'a su amfana.

Akwai wasu karin ayyuka da ake sa ran sanatan zai kaddamar a 'yan kwanaki masu zuwa.

Wasu na ganin wannan yunkuri da Sanata Melaye ke yi na da alaka da zabukan 2019, musamman yadda yake takun-saka da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC, wacce a tutar ta ne aka zabe shi.

Sai dai alamu na baya-bayan nan sun nuna cewa ba zai ci gaba da zama a jam'iyyar ba.