Yadda sakon WhatsApp ya jawo kashe-kashe a wani kauye

Mohammad Salman
Image caption An yi wa Mohammad Salman duka sakamkon jita-jitar da aka rika yi kan cewa shi mai satar yara ne

Wani Ba'Indiye mai shekara 32 wanda injiniyar kwamfuta ne ya kasance mutum na baya-baya nan daya fada hannun gungun mutane masu daukar doka a hannunsu, sakamakon zargin satar yara da aka yi masa wanda aka yada a shafin sada zumunta na WhatsApp.

Wakiliyar sashen Telegu na BBC Deepthi Bathini ta rubuta rahoto kan yadda al'amarin ya faru.

"Sun rika dukanmu, inda suka bukaci mu fada musu yawan yaran da muka sace," in ji Mohammad Salman, wanda har yanzu yana cikin dimuwa.

Kuma sai da aka dinke wuraren da Salman ya ji raunuka a jikinsa da kuma fuskarsa.

A ranar 13 ga watan Yuli ne, wani gungun mutane ya yi wa Salman, mai shekara 22, da abokansa biyu duka na fitar hankali bisa zargin satar yara.

Abu na karshe da ya tuna shi ne lokacin da aka rinka jan abokinsa Mohammad Azam da igiya da aka daure a wuyarsa.

Sai dai abokin nasa bai yi sa'a ba, don ya rasa ransa daga karshe sakamakon raunukan da ya ji.

Mutanen uku sun kai ziyara gidajen danginsu da ke Handikera ne, wanda wani karamin kauye ne da ke kewaye da filayen gonaki a jihar Karnataka da ke kudancin kasar.

Suna zaune ne a babban birnin jihar Telangana. Sun yi tattaki ne da mota zuwa kauyen tare da wasu abokansu su biyu domin su yi kwanaki a can.

Sai dai sa'o'i bayan isowarsu, an bayanna dukkaninsu su biyar a matsayin masu satar yara kuma mazauna kauyen sun kai musu hari bayan da suka fusata.

Hutun karshen mako da suka je yi, ya zama wani abin tashin hankali.

'Yan sanda sun kama mutane 22 ciki har da mutumin da ya bude wani dandali a shafin WhatsApp.

Har ila yau 'yan sadan sun ce sun cire wasu shafuka 20 da wasu suka bude a WhatsApp domin dakile sake aukuwar hakan.

"Akwai bidiyon da ya shigo hannunmu wanda shaidu suka dauka kuma mun duba su daya bayan daya. Mun yi nazari kan bidiyon domin mu tabbatar mun tantance wadanda suka kai harin da kuma wadanda suka rika ba su kariya," in ji wani babban jami'in dan sanda.

Dan sandan ya ci gaba da cewa: "Idan mun gano karin wasu, toh za mu kama su."

Mutum akalla 17 ake zargin an kashe a Indiya kan zargin satar yara daga watan Afrilu zuwa yanzu.

A dukannin mutanen da aka kashen, 'yan sanda sun ce an yi hakan ne bayan yada jita-jitar ta sakonin da aka tura ta shafin WhatsApp.

Masu bincike sun ce a mafiya yawan lokutan mutane kan tura da sakonin karya ko kuma hotonan bidiyo bogi zuwa ga sauran mutane da suke mu'amala da su a dandalin sada zumunta, inda wasu suna da mabiya fiye da 100.

Daga nan ne cikin sauri sai gungun mutane su taru domin kai wa baki hari, kuma 'yan sanda ba su da isashen lokacin mayar da martani.

Image caption Mohammad Azam shi ne ya rasa ransa bayan harin da aka kai musu

Hakan ya yi kama da abin da ya faru a Handikera.

Salman ya ce suna kan hanyarsu ta zuwa wani tafki ne da ke wajen kauyen lokacin da suka hango wasu yara da ke dawowa daga makaranta.

Ya ce daya daga cikin abokansa na rike da alawar cakulan kuma ya yanke shawarar raba wa wadansu yaran kauyen.

Sai dai ya yi jifa ne da alawan ta bakin ta ga saboda motar tana gudu sosai.

Salman ya ce ba su tsaya a wani wuri ba kuma sun ci gaba da tuki har sai da su ka isa tafkin.

Sun fitar da kujeru da suka zo da su daga cikin mota domin su zauna kuma su huta.

"Kafin mun san abin da ke faruwa, mazauna kauyen sun taru a gabanmu kuma sun rika zarginmu da satar yara," in ji Mohammad Afroz, wanda shi ma yake cikin tawagarsu Salman.

Babu cikakken bayani akan dalilin da ya sa mazauna kauyen suke zarginsu da satar yara.

"Mun rika kokarin shawo kansu amma hakan ya faskara. Sun rika jifar motarmu da duwatsu kuma har duwatsun suka fara taba abokaina"

Afroz ya kira kawunsa, Mohammad Yakub, wanda cikin hanzari ya zo wurin amma mazauna kauyen suka ki saurararsa.

Image caption Motar ta kife lokacin da gungun mutanen suka rika jifa da duwatsu

Daga bisani 'yan sanda sun gano wani hoton bidiyo da aka dauka a wayar wani mutum da ake tsammanin yana cikin gungun maharan.

Mutumin ya raba hoton bidiyon a cikin a dandalinsu na WhatsApp mai magoya baya 20.

Lokacin da Salman da Azam da kuma abokinsu, Salham Ali, suka tsere daga hannun gungun, sun arce da motarsu, gungun sun fahimci cewa sun doshi wani kauye kusa da ake kira Murki.

A cewar 'yan sanda, daya daga cikin mutanen da ke cikin gungun ya kira wani abokinsa da ke Murk kuma sun fada masa ya sa ido kan wata jar mota da ke dauke da mutane masu satar yara.

An bar Afroz da kuma mutum na biyar, Noor Mohammad, a baya kusa da tafkin amma sun tsere bayan da hankalin gungun mutanen ya koma kan motar da ta tsere.

"Mun dauka an shawo kan batun kuma za mu hadu da sauran a cikin kankanin lokaci," in ji Afroz.

"Sai dai a cikin minti biyar, wani ya kira ni yana fada mani cewa motarsu ta fada cikin wani rami a Mukri."

Salman ya ce daga nan ne mazauna kauyen sun toshe hanyoyi da ita ce, kuma saboda tsananin gudun da suke yi, motar ta kubuce daga hannunsu lokacin da suka yi kokarin kauce ma shingen.

"Sun rika jifar motar da duwatsu kuma sun fasa tagunan motar da sanduna da kuma duwatsu. An yi amfani da karfi wajen fitar da ni kuma an doke ni sosai ," in ji shi.

"Sun kai mana hari da wukake da kuma sanduna. Har da mata a cikin gungun mutanen."

Wani hoton bidiyon da wani da ya shaida lamarin ya mika wa jami'an 'yan sanda ya nuna mutane da suka fusa ta sun kewaye motar da ta kife, Wani dan sanda ya rika ba mutanen hakuri a kan su kyale bakin, amma hakan ya ci tura.

Image caption Garin Mukri, wurin da lamarin ya faru

Salman ya kara da cewa shi da abokinsa, Ali, sun tsira ne saboda 'yan sanda sun boye su a bayan motarsu domin ba su mafaka.

Sai dai basu iya kubatar da Azam ba. Salman ya ce wasu daga cikin 'yan kauyen sun yi kokarin taimaka musu sai dai yawan jama'ar da suka fito ya fi karfinsu.

Wasu sun ce daruruwan mutane ne suka fito.

"Ina tsammanin mutanen kusan 1,000 ne suka fito," in ji Vijay Patil, wani ganau wanda yake da shagon shan shayi a Murki.

"Dukkaninmu da ke cikin dandanlin an turo mana hoton bidiyon," in ji shi, ya kuma kara da cewa a daren ranar da lamarin ya faru ya yanke shawarar barin dandalin sakamakon "irin fitinar da bidiyon da aka yada a shafin ya haddasa".

Salman ya ce gungun mutanen sun yi fiye da awa guda suna wurin kafin suka tafi bayan da aka tura da karin motocin 'yan sanda biyar zuwa kauyen.

Kafin isowarsu gungun sun riga sun raunata jami'an 'yan sanda takwas wadanda suka rika kokarin hana su.

Mallikarjun, wanda jami'in dan sanda ne da ya nemi a sakaya sunan mahaifinsa ya ce ya samu karaya a kafarsa ta hagu a daren ranar.

Ya ce ba ya iya barci tun bayan aukuwar lamarin.

"Ina tashi a firgice," in ji shi . "ina ganin fuskokin mutanen uku da ke cikin mota, sun hada hannunsu suna rokon a bar su su tsira, kuma jini na zuba a fuskokinsu."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shafin WhatsApp yana sanya talla a jaridu domin yaki da dabi'ar yada labaran karya

Gwamnatin yankin ta ce sun aiwatar da shirye-shiryen fadakar da mazauna kauyen bayan aukuwar lamarin.

"Duk da kokarin da muka rika yi, wannan lamari abin takaici ne," in ji wani jami'i.

Lamarin ya shafi harkokin yau da kullum na kauyen.

Yawan al'ummar Murki ya kai 5,000 kuma wuri ne da babu hayaniya.

'Yan sanda sun ce ba su da kayan aikin da zai ba su damar tunkarar gungun mutanen wadanda suke da yawa sosai.

Sun fi daukar mataki wajen sasanta ma'aurata da suka samu sabani da kuma takaddama a kan dukiya da kuma fada tsakanin masu shan barasa.

Labarai masu alaka

Karin bayani