Ambaliyar Katsina: Ruwa ya tafi da jaririya 'yar wata uku

  • Mansur Abubakar
  • BBC News Pidgin, Kano
Masari

Asalin hoton, Twitter/@GovernorMasari

Labarai masu sosa rai sun fara fitowa daga garin Jibiya na jihar Katsina yayin da mutane ke neman 'yan uwa da abokan arziki a garin na arewacin Najeriya.

Wakilin BBC ya shiga garin da aka yi ambaliyar ruwa domin gane wa idonsa irin iftila'in da ya fada wa mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Ruwa ya tafi da jaririya

Wani magidanci ya shaida wa BBC cewar da matarsa ta haifu, ya yi murna matuka saboda 'yarsa ta farko kenan a duniya. Ya kuma rada mata suna, Fatima Attahir.

Sai dai kuma ransa ya baci a lokacin da ambaliyar da aka yi ta tafi da jaririyar tasa wadda ba ta wuce wata uku ba a duniya.

Abin da ya dada tsananta bacin ransa shi ne hoto daya tilo da ya dauki jaririyar tasa yana cikin wayarsa, kuma ambaliyar ta tafi da wayar.

Amma abin da yake rage mishi radadin rashin shi ne kasancewar matarsa da rai da kuma fatan cewa za su sake haihuwa nan gaba.

Wata mata da 'ya'yanta uku

Ambaliyar ta kuma tafi da wata mata da 'ya'yanta uku.

Matar dai ta kasance tana zama da 'ya'yanta a gida ne tun da maigidanta ya rasu a shekarar da ta gabata.

Makwabtanta sun shaida wa BBC cewar bayan an fara ambaliyar kowa na arce wa domin neman tsira.

Sai dai kuma da suka isa tudun mun tsira, sai suka fara jin ihun matar da 'ya'yanta.

Da jin haka, sai suka daura wata igiya a jikin bishiya kuma suka wurga wa matar igiyar domin ita 'ya'yanta su kama domin ficewa daga ambaliyar.

Sai dai kuma ambaliyar na da karfi sosai, abin da ya sa matar ta kasa rike igiyar. Saboda haka ruwa ya tafi da ita da 'ya'yanta uku.

Daga baya ne aka samu gawarwakinsu kuma aka bunne su.

Bayanan hoto,

Most of those we im save na im nebors

Amarya ba ta ji dadin aure ba

Wata sabuwar amaryar da aka yi wa aure ranar Juma'a ba ta mori amarci ba kafin ambaliyar.

Bayan an daura aurenta ranar Juma'a, ranar Asabar aka kai ta gidan mijinta, kuma ranar Lahadi aka fara ruwan da ya janyo ambaliyar.

Amaryar na cikin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan.

Wadanda suka halarci daurin aurenta sun ce abin da ya faru da matar na cikin abubuwan da suka fi damunsu.

Bayanan hoto,

Sani Yahaya ya sami gawar matarsa a garin Madarumfa na Jamhuriyar Nijar

Wani dattijo ya rasa gidansa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wani dattijo, Mallam Sule Jibiya, ya tsira da ransa. Sai dai kuma muhallinsa bai tsira ba.

Dattijon ya shaida wa BBC cewar shekarunsa sun dara 70 kuma gidan da ya rasa ne muhallinsa daya tilo.

Ya ce "Da na kalli abin da ya rage a muhallina, ga yadda shekaruna suke yanzu, ta yaya zan iya samun karfin gina wani gida. Gwamnati ta taimaka min."

Mutumin ya kara da cewa babu wanda zai iya taimaka masa a cikin 'ya'yansa.

Kawo yanzu dai mutane sun tare a makarantar Firamaren Jibiya inda ta koma sansanin 'yan gudun hijira na wucin gadi, sai dai kuma wadanda suke wurin suna korafin cewar ba sa samun abinci da sauran kayayyakin da suke bukata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadinsa kan lamarin da ya faru a jihar, wacce nan ce mahaifarsa.

Kuma tuni mataimakinsa Yemi Osinbajo ya kai ziyara yankin domin jaje, sannan ya yi alkawarin ganin an kai wa mutanen daukin gaggawa.

Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya tabbatar da cewa mutum 44 ne suka rasu a ambaliyar, inda ake cigaba da neman mutum 20.