Birtaniya na fuskantar matsin lamba daga Tarayyar Turai kan Brexit

Theresa May

Asalin hoton, AFP/getty

Bayanan hoto,

Firai ministar Birtaniya Theresa May

Ministoci daga dukkan kasashen Turai 27 za su hallara a birnin Brussels domin tattauna batun ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

Ana sa ran ministocin za su tattauna ne kan wani rahoto na musamman da Firai minista Theresa May ta fitar kan batun da ake kira Brexit.

An so a gudanar da wannan taron na ministoci daga kasashe 27 na Tarayyar Turai tun farkon wannan makon, amma rikita-rikitar siyasar Birtaniya ta sa aka dage shi zuwa yanzu.

Wani dalili kuma shi ne kasashen na Turai sun nemi a ba su isasshen lokaci domin su duba sauye-sauyen da aka samu a jami'ai masu jagorantar wannan muhimmin aiki daga bangaren Birtaniya, bayan David Davis ya sauka daga mukamin.

Babban jami'in Tarayyar Turai akan batun na Brexit, Michel Barnier, zai sanar da ministocin yadda ganawarsa da sabon Sakataren da ya maye gurbin Mista David Davis ta kasance.

Mista Domic Raab ya gaji wannan mukami a lokaci mai matukar sarkakiya a siyasar Birtaniya, amma ya yi alkawarin samar da sabuwar hanyar da za ta kasance ta sha bamban da wadda ake bi a da.