Trump ya gayyaci Putin zuwa Amurka

US president Donald Trump shakes Russian counterpart Vladimir Putin's hand

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Donald Trump da Vladimir Putin na gaisawa a Helsinki

Shugaban Amurka Donald Trump ya gayyaci shugaban Rasha Vladimir Putin ya ziyarci Amurka, inji kakakin shugaban Amurka.

Sarah Sanders ta bayyana haka ne a cikin wani sakon Twitter da ta aika, kuma ta ce tuni ana can ana tattaunawa game da wannan ziyarar.

Tun da farko dai Mista Trump ya ki amincewa da wani wani roko da Rasha ta yi na neman a ba ta izinin tambayar wasu Amurkawa abin da suka sani game da batun kutse a zaben Amurka.

Shugabannin biyu sun gudanar da wani taron koli a kasar Finland ranar Litinin, amma babu cikakken bayani game da batutuwan da suka tattauna akai.

Kawo yanzu Rasha ba ta ce uffan ba game da wannan gayyata.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Shugaban 'yan majlisar dattawan Amurka daga jam'iyyar Democrat, Chuck Schumer ya yi kira ga Mista Trumpo da ya bayyana dukkan abubuwan da suka tattaunawa da Mista Putin.

Ya kara da cewa: "Idan ba mu san ainihin abin da suka tattaunawa akai ba a birnin Helsinki, bai kamata shugaba Trump ya cigaba da dukkan wata hulda da Mista Putin ba, ko a Amurka ko ma a ina ne cikin duniya."