Kotu ta soke waranti kan tsohon shugaban Kataloniya

Carles Puidgemont

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsohon shugaban yankin Kataloniya Carles Puidgemont

Wani alkali a Spaniya ya janye warantin da aka fitar a fadin Tarayyar Turai da ta umarci a kama tsohon shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont.

Warantin ta hada da wasu jami'ai biyar da suka taka rawar samar ma yankin 'yancin kai daga Spaniya.

An dai kama Mista Puidgemont ne a Jamus.

Wata kotu a can ta yanke hukunci cewa za a iya tasa keyarsa zuwa Spaniya domin tuhumar da ake masa na almubazzaranci da kudaden al'umma.

Tuhumar ta na nuni ne da lokacin da aka gudanar da kuri'ar raba gardama a yankin Kataloniya a watan Oktobar bara wanda kotunan Spaniyar suka ce an yi shi ba bisa ka'ida ne ba.

Amma kotun ta Jamus ba ta amince da a koma da shi kasarsa ba saboda tuhumar tada kayar baya, saboda ta ce ba ta same shi da wannan laifin ba.

Saboda haka a yanzu Mista Puidgemont da da sauran jami'an tsohuwar gwamnatin yankin Kataloniya na da 'yancin yi tafiye-tafiye.

Uku a cikinsu: Toni Comin, da Luis Puig, da kuma Meritxell Serret na kasar Belgium da zama a halin da ake ciki.

Ita kuwa Marta Rovira ta tsere ne zuwa Switzerland. Ta biyar kuma a cikinsu, Clara Ponsati, na Scotland.