Babu sojan da aka tsare - Gwamnatin Kamaru

Burning village in Cameroon

Gwamantin Kamaru ta musanta rahotannin an kama sojojin kasar 4 bayan bullar wani bidiyo da ya nuna sojoji sun hallaka wata mace da jaririnta da kuma wata karamar yarinya.

A makon da ya gabata ne dai bidiyon ya bulla, da janyo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta.

A cikin bidiyon an jiyo muryar sojin na zargin matar na da alaka da mayakan kungiyar Boko Haram.

Gwamnatin Kamaru dai ta yi watsi da bidiyon, tare da cewa na bogi ne amma ta yi alkawarin gudanar da bincike.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty Internatinal ta ce akwai kwarararn hujjoji da ke nuna tabbacin mutanen da ke bidiyon 'yan kasar ne.

Daman kungiyoyin kare hakkin dan adam na korafin kan sojoji na take hakkin bil'adam a yakin da suke yi da masu tsaurin ra'ayi na kunguiyar Boko Haram da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai.

Sai dai hukumomin basu kara cewa komai kan hakan ba, amma mai magana da yawun gwamnatin ya shaidawa BBC cewa zai yi karin bayani kan batun a yau Jumma'a.