Har yanzu ni dan jamiyyar APC ne - Gwamna Samuel Ortom

Governor Samuel Ortom Hakkin mallakar hoto FaceBook/Samuel Ortom
Image caption Samuel Ortom yana takun-saka ne da Sanata George Akume

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ce har yanzu shi dan jam'iyyar APC mai mulki ne'yan kwanaki bayan da ya ce ya raba-gari da ita.

Gwamnan ya yi amai ya lashe ne bayan tattaunawar sulhu da suka yi da tsohon gwanan jihar Benue George Akume karkashin jagorancin Shugaban jamiyyar Adams Oshiomhole a ranar Alhamis.

A ranar Litinin gwamnan ya bayana cewa sun yi hannun riga da jam'iyyarsa ta APC kuma ya ce ya fice daga cikinta.

Gwamnan ya kuma gana da wasu shugabannin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a ranar Laraba a jihar Kwara.

Sai dai uwar jamiyyar APC ta maida martini cikin gaggawa inda ta ce basu raba-gari da gwamnan ba, sannan ta gayyace shi da kuma tsohon gwamnan jihar Benue Senataor George Akume zuwa sakatariyar jam'iyyar domin su yi tattaunawar sulhu.

Rahotanni sun ce bayan isowarsa ofishin Jam'iyyar gwamnan ya ce ya zo ne domin su yi sulhu.

"Na zo ofishin jami'yyar APC a matsayi nan a dan jam'iyyar APC, kuma har yanzu ina rike da tutar jam'iyyar. Na ce mun yi hannun riga da jamiyyar APC amma uwar jam'iyyar ta yi min gyra," in ji shi

"Mun raba-gari da Jamiyyar APC ta jihar Benue kuma shi yasa na ga ya dace na fice sai dai shugabannin uwar jam'iyyar sun ce matakin da uwar jam'iyyar ta dauka ya fi duk wani mataki da wani ko wasu za su dauka a cikin jiha kuma a gani na wannan ya yi dai - dai".

Jami'yyar dai na fama da rikice-rikice a sassan kasar da dama, lamarin da ya kai ga bullar wani bangaren rAPC da ya yi ikirarin yin tawaye tare da kafa nashi tsarin shugabancin.

Bangaren, wanda ke karkashin jagorancin Buba Galadima, na samun goyon bayan wasu gaggan jam'iyyar da ke rike da mukamai a matakai daban-daban.

Wannan sabuwar rigimar da ta sake tasowa jam'iyyar a Benue na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar zabe ta bayyana APC a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna mai muhimmanci da aka gudanar a jihar Ekiti.

Masu sharhi na ganin idan har jam'iyyar ba ta yi sauri wurin dinke wannan baraka ba, to hakan zai iya bai wa sauran 'ya'yanta da ke kan katanga kwarin gwiwar ficewa daga jam'iyyar a daidai lokacin da ya rage watanni a gudanar da zabukan kasa baki daya.

Wadanda suka fice daga APC a kwanan nan

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Jam'iyyar APC ta kauce hanya - Buba Galadima
  • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
  • Suna dai samun goyon bayan Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi
  • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
  • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa - kamar yadda Daily Trust ta rawaito
  • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
  • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.